Jiha a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
Katsina jiha ce a shiyyar Arewa Maso Yammacin Najeriya.[1] An kuma ƙirkiri jihar Katsina ne a shekarar 1987, lokacin da aka samar da ita daga jihar Kaduna. A yau, Jihar Katsina ta yi iyaka da Jihohin Zamfara da Kaduna da Kano da Jigawa, har ila yau Kuma Katsina tanada iyaka da Jamhuriyar Nijar. Ana yi mata laƙabi da "Ta Dikko Ɗakin Kara", kuma ana yi wa Katsinawa kirarin "Kunya gareku ba dai tsoro ba".Babban birnin jihar da garin Daura, an bayyana su daga cikin "tsofaffin mazaunun al'adu da Musulunci da kuma ilmantarwa" a Najeriya.
Katsina | |||||
---|---|---|---|---|---|
Katsina State (en) Jihar Katsina (ha) | |||||
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Katsina | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 7,831,319 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 323.72 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 24,192 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Kaduna | ||||
Ƙirƙira | 23 Satumba 1987 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina | ||||
Gangar majalisa | Katsina State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-KT | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | katsinastate.gov.ng |
Jihar Katsina, tana da mazauna sama da 5,800,000 a ƙidayar shekarar 2006, Jihar Katsina ce ta biyar mafi girma a Jerin yawan haɓakar jama'a a jihohi biyar mafi girma a cikin ƙasar ta Nijeriya, cikin yawan jama'a, duk da kasancewarta ta bakwai daga cikin Jihohi 17 mafi faɗin ƙasa daga cikin jihohi 36 na tarayyar Nijeriya. Ta fuskar adadin ƙabilu kuwa, jama'a, Fulani sun fi kowace ƙabila yawa a jihar, kuma mafi yawancin mutanen Jihar Katsina suna bin koyarwar addinin Musulunci. A shekarar 2005, [2] A shekarar 2005,[3][4]Katsina ta zama jiha ta biyar a Najeriya da ta yi amfani da tsarin Shari'ar Musulunci.
Gwamnan jihar Katsina na yanzu shi ne Dr.Dikko umar radda, dan jam’iyyar "All Progressives Congress"Ana ɗaukar Jihar a matsayin babbar cibiyar siyasar Muhammadu Buhari, ɗan asalin garin Daura, wanda ya lashe a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019 da kusan kashi 80% na ƙuri’un mutanen jihar. [5]
Jihar Katsina na ɗaya daga cikin Jihohin Najeriya da ke fama da matsalar ta'addanci. Wacce ta fara a shekarar 2020. Kungiyar yan ta'adda da yan fashi da garkuwa da mutane sun yi garkuwa da yara sama da 300 a ƙaramar hukumar kankara.[6][7]
Fulani sun fi kowace kabila yawa.[2]
Galibin mutanen Jihar Katsina musulmai ne,[8][9]Samfuri:Clarify The Church of Nigeria has a Diocese of Katsina.[10] kuma Gobarau Minaret muhimmin gini ne a birnin Katsina (kuma tarihi ya tabbbatar da cewa an ginata ne domin amfanin addinin musulunci). Jihar Katsina, har yanzu tana aiwatar da Shari'a a duk faɗin jihar. Akwai kuma Cocin na Najeriya yana da Diocese na Katsina. Cocin Redeemed Christian Church of God da Cocin Roman Katolika suna nan a cikin jihar.[11]Samfuri:Failed verification[12]
Jihar Katsina ta ƙunshi kananan hukumomi har talatin da huɗu (34) ga su nan kamar haka:
Jihar Katsina cibiya ce ta ilimin boko dana yau da kullum. A halin yanzu tana da kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Katsina,[13] is a public university owned by the state government. Al-Qalam University, the first Islamic university in Nigeria is privately owned. Federal University, Dutsin-Ma[14] is owned by the federal government as well as Federal College of Education, Katsina[15] (affiliated to Bayero University Kano[16]). Kwalejin Kimiyya ta Kwalejin Hassan Usman Katsina, da Kwalejin ilimi ta tarayyar Najeriya Federal Polytechnic Daura[17] da Jami'ar myTarayya ta Dutsin-Ma, jami'ar gwamnatin tarayya ta jihar katsina, wadda aka sauya mata suna zuwa marigayi Shugaba ƙasa Umaru Musa Yar' adua, Jami'yar Umaru Musa Yar'adua, Jami'ar Alqalam ta Katsina Yusufu Bala Usman College of Legal, and General Studies, Daura da Makarantar Nazarin Karatu da Gyara, Funtua (SBRS / ABU Funtua) da Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita Dutsin-Ma, da ke garin Dutsin-ma.
A takaice dai akwai cibiyoyin bayar da digiri har guda bakwai a cikin jihar mallakar hukumomi daba-d.a. Cn cibiyoyin sune Jami'ar Umaru Musa Yar' adua[18], mallakar gwamnatin jihar. Jami'ar Alqalam Katsina, jami'ar Musulunci ta farko a Najeriya kuma mallakar ta ce. Jami'ar Tarayya ta Dutsinma, mallakar gwamnatin tarayya. Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Katsina (wacce ke da alaƙa da Jami'ar Bayero ta Kano). National Open University of Nigeria, Isa Kaita College of Education Dutsinma (wacce ke da nasaba da Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya), kwalejin ilimi ce ta jihar. Cibiyar Cherish Batsari, wata jami'a mai zaman kanta ta ba da digiri a kwasa-kwasan kiwon lafiya. [19]
Duk da matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka na hana yaɗuwar cutar COVID-19 a cikin jihar, a ranar bakwai ga watan Afrilu shekerar dubu biyu da shirin (2020).Wani likita a karamar hukumar Daura ya mutu sakamakon kamuwa da cutar da ke da alaƙa da Corona virus kuma an yi wa dangin sa gwaji mai kyau. Daga baya, daya daga cikin majiyyatan likitan shima ya mutu. Don dakile yaduwar cutar, gwamnatin jihar ta bada umarnin kulle a cikin jihar tare da tura 'yan sanda don tabbatar da bin doka. Ko yaya, akwai lokuta da suka saba wa wannan umarni kuma mutane na zargin gwamnati da kulle wuraren ibada kamar su coci-coci da masallatan Juma'a yayin da manyan kasuwanni irin su 'Yar Kutungu, Himata, Greenhouse, Mudassir da sauransu ke aiki. An yi arangama tsakanin ‘yan sanda da matasa a karamar hukumar Kusada wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kame fararen hula.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.