Neja
jiha a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
jiha a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
[[File:Zuma rock niger state Uku 3( on transit ).jpg|thumb|Dutsen Zuma kenan na jikin Naira dubu dake a niger]]
Neja | |||||
---|---|---|---|---|---|
Niger (en) | |||||
| |||||
| |||||
Suna saboda | Nijar | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Minna | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 5,556,247 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 72.76 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 76,363 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Arewa Maso Yamma | ||||
Ƙirƙira | 3 ga Faburairu, 1976 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | executive council of Niger State (en) | ||||
Gangar majalisa | Niger State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-NI | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | nigerstate.gov.ng |
Jihar Neja Jaha ce dake Arewa[1] ta tsakiyar Najeriya[2]. Tana da yawan fili kimanin kilomita dubu saba'in da shida da Dari uku da sittin da uku (76,363 ), da yawan jama’a kimanin miliyan uku da dubu dari tara da hamsin da hudu Du da dari bakwai da saba'in da biyu, kidayar yawan jama'a na shekara ta dubu biyu da shida(2006).Babban birnin jahar shine Minna[3].
Jihar Neja na cikin jihohi talatin da shida 36, na Najeriya Takenta shi ne '"Power State"' saboda tana da madatsun ruwa guda uku (3) da ke samar da kusan kashi saba'in 70% na wutar lantarkin Najeriya.
An kafa jihar Neja ne a ranar uku 3 ga watan Fabrairun shekarar dubu daya da dari tara da saba'in da shida 1976 daga rusasshiyar jihar Arewa maso Yamma a zamanin mulkin Janar Murtala Mohammed.
Jihar tana a shiyyar arewa ta tsakiya mai yanki mafi girma wanda ya kai kusan 80000km2, tare da kusan kashi saba'in 70% na gonaki da noma. Jihar Neja tana iyaka da Jihar Zamfara ta bangaren Arewa, Yamma da Jihar Kebbi, Kudu da Jihar Kogi, Kudu maso Yamma da Jihar Kwara, Arewa maso Gabas da Jihar Kaduna da kuma Kudu maso Gabas da Abuja. Haka kuma jihar tana da iyaka ta kasa da kasa da jamhuriyar Benin tare da kananan hukumomin Agwara da Borgu zuwa Arewa maso Yamma.
Jahar ta Neja tana da manyan mutane da dama wadanda suka rike manyan mukamai a kasar Najeriya sannan jiha ce wacce ta ke da tsofaffin shugabannin kasa na Najeriya har guda biyu a lokacin mulkin soja, wato Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) mai ritaya da kuma Abdusalami Abubakar mai ritaya dukkaninsu mutanan Jahar ta Neja ne.[4][5]
Manyan kananan hukumomin Jahar su ne kamar haka: Chanchaga, Bosso da kuma kananan hukumomin Bidda, Suleja da kuma Kontagora.
Manyan yarukan jihar sun haka ne da Nufanchi, Hausa, Gbagi da kuma turanci inda yankunan Bidda da Agaie da kuma Lapai, Mokwa suka fi yawan masu amfani da yaren Nufanci, Yankin Kontagora, Kagara, Mariga, Mashegu Rijau, Suleja suke da mafi rinjayen masu amfani da yarukan Hausa. Paikoro, Chanchaga, Bosso, Edati da dai sauransu suna amfani da saura yarukan a matsayin masu rinjaye.
Akwai wuraren tarihi sosai a jahar ta Neja musamman a garin Zungeru inda kuma a nan ne turawan Yamma suka saka hannu domin hadewan Najeriya kasa daya daga sauran yankuna sannan a wannan garin ne gwamnan farko na Najeriya ya yada zango a matsayin hedikwata gareshi.
Alhaji Umar Farouk Bahago shi ne sarkin Minna.
Jihar Neja tana da iyaka da misalin jahohi shida, sune: Babban birnin tarayya, Kwara, Kogi, Kaduna(jiha)|Kaduna]], Kebbi kuma da Zamfara.[6]
Jerin sunayen Gwamnonin jihar Neja. https://en.m.wikipedia.org/wiki/List_of_governors_of_Niger_State
Jihar Neja tana da kananan Hukumomi guda ashirin da biyar (25). Sune:
Jihar Neja na da manyan jami'oi na ilimi wadanda suka hada da:
Sanannun mutane na jihar Neja sun hada da :
An jero yarukan jihar Neja dangane da ƙananan hukumomin da ake amfani da su;[18]
LGA | Languages |
---|---|
Agaie | Nupe, Dibo; Kakanda; |
Agwara | Cishingini |
Bida | Nupe, BassaNge, Gbari |
Borgu | Busa, Bisã; Boko; Cishingini; Laru; Reshe |
Chanchaga | Basa-Gumna; Bassa-Gurmana; Gbagyi; Gbari; Nupe; Kamuku; Tanjijili |
Edati | Nupe, BassaNge |
Gbako | Nupe |
Gurara | Gwandara, Gbagyi |
Katcha | Nupe, Dibo; Kupa |
Kontagora | Acipa, Eastern; Asu; Tsishingini; Tsuvadi |
Lapai | Nupe, Dibo; Gbari; Gupa-Abawa; Kakanda; Kami; |
Magama | Lopa; Tsikimba; Tsishingini; Tsuvadi |
Mariga | Baangi; Bassa-Kontagora; Cicipu; Kamuku; Nupe; Rogo; Shama-Sambuga; Tsikimba; Tsishingini; Tsuvadi |
Mashegu | Asu; Tsikimba; Tsishingini; Nupe-Tako |
Minna | Nupe; Gbari; Gbagyi |
Mokwa | Nupe, Yoruba; Gbari |
Munya | Adara |
Paikoro | Gbari; Kadara |
Rafi | Basa-Gurmana; Bauchi; Cahungwarya; Fungwa; Gbagyi; Gbari; Kamuku; Pangu; Rogo; Shama-Sambuga |
Rijau | Fulani; C'Lela; Tsishingini; Tsuvadi; ut-Hun |
Shiroro | Gbagyi; Gurmana; Bassa |
Suleja | Gbagyi; Gbari; Gwandara; Nupe; Tanjijili |
Wushishi | Hausa; Nupe; Gbari |
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.