Remove ads
Jihar ce a arewa maso gabashin Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
Yob Arewacin Najeriya Yobe jiha ce daga cikin jerin jihohin shiyyar Arewa[1] Maso Gabashin Najeriya.[2] [3]Tana da yawan kasa kimanin murabba'in kilomita 45,502 da yawan jama’a miliyan ɗaya da dubu dari hudu da sha- daya da dari hudu da tamanin da ɗaya "1,411,481" (a kidayar yawan jama'a ta shekarar 1991).[4] [2]Babban birnin jihar shi ne Damaturu. Mai Mala Buni[5] shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta dubu biyu da goma sha biyar 2015 zuwa yau[6]. Mataimakin[7] gwamnan shi ne Idi Barde Gubana[8].Jihar dai tana da bangarori guda uku: bangaren gabas, kudu da kuma arewa[7].'yan majalisar Dattijan jihar su ne: Ahmed Ibrahim Lawan[9] mai wakiltar shiyyar arewaci, Bukar Abba Ibrahim Ibrahim Gaidam[10] shiyyar gabashi da, Ibrahim Mohammed Bomai shiyyar kudanci.
Yobe | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Suna saboda | Komadugu Yobe | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Damaturu | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,294,137 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 72.4 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 45,502 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Komadugu Yobe | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Borno | ||||
Ƙirƙira | 27 ga Augusta, 1991 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | executive council of Yobe State (en) | ||||
Gangar majalisa | Majalisar dokokin Jihar Yobe | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-YO | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | yobestate.gov.ng |
Jihar Yobe tana da iyaka da jihohi hudu, Kamar haka: Bauchi, Borno, Gombe da kuma Jigawa. Tana kuma da iyaka da jamhuriyar Nijar.[3]
An kirkiri jihar Yobe ne a ranar 27 ga watan Agustan 1991.[11] An ciro ta ne daga jihar Borno a zamanin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida kuma an yi hakan ne don a sauƙaƙa sha'anin tafiyar da mulki a yankin. Ranar 14 ga watan Mayun 2013, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya rattaba dokar ta baci a jihar Yobe da Borno da kuma Adamawa. Saboda harin ta'addanci na kungiyar Boko Haram . Karkashin Abubakar Shekau, shugaban kungiyar ta Boko Haram, haifaffen kauyen Shekau ne na jihar Yobe.
Jahar Yobe tana da kananan hukumomi guda goma sha bakwai (17) wadanda suka hada da:
Wadannan su ne harsunan mutanen Jihar da kuma kananan hukumomin da ake samun su:[12]
Kananan Hukumomi | Harsuna |
---|---|
Bade | Bade; Duwai |
Bursari | Fulbe Bade |
Damaturu | Kanuri; Fulani |
Fika | Karaikarai; Ngamo; Fulani Bolewa |
Fune | Fulani,Abore |
Geidam | Kanuri |
Gujba | Fulani,Kanuri, |
Gulani | Maaka, Fulani |
Jakusko | Fulani, Bade, |
Nangere | Karai-karai da fulani |
Nguru | Kanuri; Hausa; Bade |
Potiskum | Karai-karai, Ngizimawa, bolawa |
Tarmuwa | Fulani, kanuri |
Yunusari | Kanuri, Fulani |
Yusufari | Kanuri, Fulani |
Machina | Mangawa |
Sauran harsunan da ake samu a jihar Yobe sun haɗa da Baburawa, Mangawa da kuma Zarmawa da kuma Fulani da kuma ngizim da kuma Kare-kare.[12]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.