Gombe jiha ce dake Arewa maso Gabashin Najeriya. Tayi iyaka daga Arewa da Arewa maso gabas da jihohin Borno da Yobe, daga Kudu kuwa da Jihar Taraba, daga Kudu maso yamma kuwa da Jihar Adamawa sannan daga Yamma da Jihar Bauchi. Ta samo asalin sunanta daga babban birninta kuma yanki mafi girma a jihar wato Babban Birnin Gombe - kuma an ƙirƙireta ne daga sashin Jihar Bauchi a ranar daya ga watan Oktoba shekara ta alif dubu daya da ɗari tara da cassa'in da shida 1996. Jihar na daga cikin jihohin da ke ɗauke da ƙabilu iri-iri a Najeriya. Acikin jihohi talatian da shifa 36, da Abuja na Najeriya, Jihar Gombe itace Jiha ta ashirin da daya 21, a girma, kuma ita ce ta talatin da biyu 32, a yawan jama'a, da mutane aƙalla ya kai kimanian miliyan uku da dugo ashirin da biyar 3.25, dangane da ƙiyasin shekara ta dubu biyu da sha shida 2016.[1]

Quick Facts Suna saboda, Wuri ...
Gombe
Thumb
Thumb

Suna saboda Gombe
Wuri
Thumb Thumb
 10°15′N 11°10′E
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Gombe
Yawan mutane
Faɗi 3,256,962 (2016)
 Yawan mutane 173.54 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 18,768 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Bauchi
Ƙirƙira 1 Oktoba 1996
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Gombe State (en) Fassara
Gangar majalisa Gombe State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-GO
Wasu abun

Yanar gizo mof.gm.gov.ng
Kulle
Thumb
Thumb
Jihar gombe
Thumb
Sarkin gombe
Thumb
gombe post ofis
Thumb
wajan tirenin a gombe
Thumb
Governor of Gombe State. Muhammad Inuwa Yahya
Thumb
Muhammad Damjuma Goje. Passed Governor of Gombe State and Current Senator
Thumb
Ibrahim Hassan Dankwambo. Passed Governor of Gombe State and Current in House of Assembly
Thumb
Abubakar Shehu-Abubakar The current Emir of Gombe State
Thumb
The late Emir of Gombe. His Royal Highness, Alhaji Shehu Usman Abubakar From January 1984 to May 2014
Thumb
Gombe United FC
Thumb
President John F. Kennedy visits with members of Parliament of Nigeria in the West Wing Colonnade of the White House, Washington, D.C. The Parliamentary delegation includes: President of the Senate, Dennis Chukude Osadebay; Speaker of the House of Representatives, Ibrahim Jalo Waziri; Deputy Speaker of the House of Representatives, Emmanuel Chikere Akwiwu; members of the Senate, Dahlton O. Asemoto, Chief Z. C. Obi, and Zanna Medalla Sheriff; members of the House of Representatives, Mallam Muhammadu Sagir Umar and Chief Ohu Babatunde Akin-Olugbade; Staff Assistant to the delegation, J. O. Adeigbo.
Thumb
Sheikh Kabiru Haruna Gombe
Thumb
Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Thumb
Amina J. Mohammed
Thumb
Issa Ali Pantami

Ta fuskar yanayin ƙasa, Jihar tana da ƙasa nau'in wuraren zafi a yammacin Sudanian Savanna. Muhimman wurare a jihar sun haɗa Kogin Gongola, wanda ke kwarara ta arewaci da Gabashin Gombe zuwa cikin tafkin Dadin Kowa Dam zuwa gaɓar Tsaunukan Muri da ke can yankin kudancin jihar. Daga cikin dabbobi asali na jihar akwai nau'in macizai addun su: carpet viper, puff adder, da kuma Egyptian cobra da kuma dabbobi irin su dorinar ruwa, Senegal parrot, da kuma grey-headed kingfisher.

Jihar Gombe na ɗauke da ƙabilu da dama, yayinda Ƙabilar Fulani suka mamaye yankin arewaci da tsakiyar jihar tare da Bolewa, Kanuri, da kuma Hausawa. A yayin ƙabilu irin su Cham, Dadiya, Jaranci da Kamo, Pero, Tangavle, Tera, da kuma mutanen Waja da suka mamaye yankunan gabashi da kudancin jihar.

Kafin zuwan Turawa, yankin Jihar Gombe ta yau tana ɗauke da ƙasashe da dama masu zaman kansu, har zuwa farkon karni na dubu daya da dari takwas 1800, lokacin da Fulani suka ƙwace yankuna da dama na yankin kuma suka haɗeta a matsayin Masarautar Gombe a ƙarƙashin Daular Sokoto. A cikin karni na dubu daya da dari tara1900, Turawan mulkin mallaka suka mamaye masarautar da yankunan gefen ta kuma sun haɗeta acikin Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya, inda daga bayan zuwan turawa Nigeria, daga bisani ta samu 'yancin kai a shekarar dubu daya da dari tara da sittin 1960, kuma ta zamo ƙasa Najeriya. Bayan samun 'yancin kai kuwa, Jihar Gombe ta yau ta faɗa ƙarƙashin Arewacin Najeriya har zuwa shekarar dubu daya da dari tara da sittin da bakwai 1967, lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta faɗa ƙarƙashin Jihar Arewa ta Gabas. Bayan an raba Jihar Arewa maso Gabas, an ƙirƙiri Jihar Bauchi a shekarar dubu daya da dari tara da saba'in da bakwai 1976, tare da Sauran jihohi guda goma. Shekaru ashirin bayan haka (1996), an cire wasu gungun ƙananan hukumomi daga yammacin Jihar Bauchi don samar da Jihar Gombe.

Dangane da fannin tattalin arziƙi, Jihar Gombe ta dogara ne akan noma da kiwo, da man fetur, inda ake shuka gero, masara, gyaɗa, dawa da tumatiri tare da kiwon dabbobi kamarsu raƙumma, shanu, akuyoyi da kuma tumaki. Sauran muhimman masana'antu sun haɗa da hidindimu na zamani da ake gudanarwa musamman a birnin Gombe. Jihar Gombe itace jiha ta huɗu a jerin ƙarancin Cigaban al'umma.

Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 18,768, da yawan jama’a miliyan biyu da dubu uku da hamsin da uku (ƙidayar yawan jama'a shekara ta dubu biyu da shida 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Gombe. Muhammad

Inuwa Yahaya [1] shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015, har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Dr Manasa Daniel Jatau. Dattijan jihar su ne: Sarakunan gargajiya, Malaman addini da kuma jigogin siyasa.[2]

Bayani.

Jihar na da faɗin fili na kimanin 20,265 kilo mita 2 da kuma mutane kimanin mutum 2,365,000, a shekara ta dubu biyu da shida 2006. An ƙirkire ta ne a cikin watan Oktoba shekarar dubu daya da dari tara da cassa'in da shida 1996, daga yankin tsohuwar Jihar Bauchi a lokacin mulkin Shugaba Sani Abacha. Jihar na nan a yankin ƙasar Najeriya mai nau'in tsirrai irin na Guinea savannah da Sudan savannah. Akwai tuddai masu ɗan bisa, duwatsun ƙasa da kuma duwatsu na daga witar volcano hkunan tsaunukan garin. Zaman jihar a yankin savanna na arewa maso gabashin Najeriya yasa jihar ta haɗa iyaka da jihohi kaman Borno, Yobe, Taraba, Adamawa da Bauchi.

Jihar Gombe ta na yanayi guda hudu:yanayin rani (daga watan fabru zuwa aprelu) da kuma damuna (daga watan mayu zuwa Oktoba) tare da matsakaicin ruwam sama na kimanin 850mm.Da Kuma hunturu (daga Watan nuwamba zuwa junairu)

Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa ke javorancin jihar tare da taimakon muƙarrabai 24, daga majalisar dokoki na jihar. Jihar Gombe na da ƙananan hukumomi 11, da kuma masarautu na gargajiya guda 14. Tana da sanatoci guda 3, da kuma 'yan Mjalisar Tarayyar Najeriya guda shida.

Ƙananan Hukumomi.

Jihar Gombe nada Kananan hukumomi guda goma sha ɗaya (11). Sune kamar haka:

Ƙarin bayanai Karamar Hukuma, Fadin kasa (km2) ...
Karamar Hukuma Fadin kasa (km2) Adadin 2006
Mutane
Cibiyar Karamar Hukuma Lambar aika
sako
Akko 2,627 337,853 Kumo 771
Balanga 1,626 212,549 Tallase 761
Billiri 737 202,144 Billiri 771
Dukku 3,815 207,190 Dukku 760
Funakaye 1,415 236,087 Bajoga 762
Gombe 52 268,000 Gombe (city) 760
Kaltungo 881 149,805 Kaltungo 770
Kwami 1,787 195,298 Mallam Sidi 760
Nafada 1,586 138,185 Nafada 762
Shongom 922 151,520 Boh 770
Yamaltu/Deba 1,981 255,248 Deba Habe 761
Kulle

Al'umma.

Jihar Gombe na ɗauke da al'ummomi iri-iri, yayinda Fulani suka mamaye mafiya yawancin yankin arewacin jihar. Fulani sun mamaye Kusan ƙananan hukumomi guda 6 na Jihar Gombe. Waɗannan ƙananan hukumomi sun haɗa da Dukku, Kwami, Funakaye, Nafada, Akko, kuma ƙaramar hukumar Gombe. Bayan Fulani akwai kuma Tangale, da ke rayuwa a yankin Billiri da Kaltungo. Sauran ƙabilu sun haɗa da the Hausawa Tula, Tera (Yamaltu-Deba), Waja, Bolewa, da kuma Kanuri.

Harsuna.

An zayyano harsunan Jihar Gombe dangane da ƙananan hukumominsu a teburi da ke ƙasa:

Ƙarin bayanai LGA, Area (km2) ...
LGA Area (km2) Census 2006
population
Administrative capital Postal
code
Akko 2,627 337,853 Kumo 771
Balanga 1,626 212,549 Tallase 761
Billiri 737 202,144 Billiri 771
Dukku 3,815 207,190 Dukku 760
Funakaye 1,415 236,087 Bajoga 762
Gombe 52 268,000 Gombe (city) 760
Kaltungo 881 149,805 Kaltungo 770
Kwami 1,787 195,298 Mallam Sidi 760
Nafada 1,586 138,185 Nafada 762
Shongom 922 151,520 Boh 770
Yamaltu/Deba 1,981 255,248 Deba 761
Kulle

Ilimi.

Jami'o'i a jihar Gombe.

Manyan jami'oi na Jihar Gombe sun haɗa da:

Makarantun Sakandiri[11]

  • Matrix International Academy[12]
  • Gombe Children and High School[13]
  • Pen Resource Academy[14][15]
  • Demonstration Secondary School
  • Government Day Science Secondary School
  • Ilimi International School
  • Gombe international School
  • JIBIWIS Arawa Secondary School
  • All-saint Secondary School
  • Darul Arqam Academy
  • Government Day Hassan Central
  • Institute for Qur'anic memorisation and Islamic civilization (IQMIC) Ma'ahad Gombe
  • Yahya Ahmad Model School[16]
  • Government Senior Secondary School Herwagana, Gombe
  • Government Senior Secondary School Gandu
  • Ubaidah Academy
  • Government Day Secondary School Gandu
  • Jibwis Islamic Science Secondary school Bolari
  • Alhidaya Academy Gombe.
  • Zaidu Bin Thabit
  • Nurul Huda International Academy
  • Nurain international school
  • Standard international school
  • Amana academy
  • Alheri model school
  • Government arabic college

Kiwon lafiya

Jihar Gombe nada cibiyoyin kiwon lafiya masu yawa, dukkanin su i sun samu ne ta karkashin gudanarwa sashi guda uku, gwamnatin jiha, Gwamnatin tarayya da kuma cibiyoyi mallakin dai-daikun mutane. Wadannan cibiyoyi sun hada da :

Cibiyoyin dake Karkashin Gwanatin Tarayya.

  • Federal Teaching Hospital Gombe (FTHG)[17]

Cibiyoyin dake Karkashin Gwamnatin Jiha.

  • Billiri General Hospital.
  • Gombe State Specialist Hospital.[18]
  • Arawa Primary Healthcare.
  • Gabukka Primary Healthcare[19]
  • Doma Primary Healthcare[20]
  • Pantami Primary Healthcare[21]
  • Zainab Bulkachuwa Women and Children Hospital[22]
  • Town Maternity (Gidan Magani).

Cibiyoyin da ba na Gwamnati ba.

  • Miyetti Hospital[23][24]
  • Musaba Hospital.
  • Savannah Hospital.
  • AHAJAS Memorial Hospital.
  • Sunnah Clinic.
  • Flossy Consultant Clinic.
  • As-sahl Hospital Gombe.
  • Dado Hospital Gombe.

Cibiyoyin Magun-guna.

  • Kumbi chemist.
  • Sauki phamarcy.
  • A.A. Aliyu Mega Store.
  • Jam Bandu Pharmacy.
  • Jam jam Pharmacy.
  • M. S. Yaro Medicine Store.

Kafofin yaɗa labarai (Gidajen Rediyo).

  • Progress FM radio[25]
  • Amana Radio
  • Gombe Media Corporation (GMC).
  • Jewel FM

Ma'adanai.

Jihar Gombe na daya daga cikin jihohi masu tarin albarkatun kasa a kasar Nigeria wanda ke samar da kayan tasarrufi da ma'aikatu ke amfani dashi, yan kasuwa ke kasuwance su, wasun kuma ake amfani dasu a matsayin abinci, wadannan ma'adanai sun hada da :

Ma'adanai da Ake Hakowa[26]

Ma'adanai da Ke Tsira.

Gwamnoni.

A ƙasa an jero sunayen gwamnoni da kuma jagorori na Jihar Gombe.

Ƙarin bayanai Name, Take ...
Name Take Lokacin hawa mulki Lokacin sauka daga mulki Jam'iyya
Group Captain Joseph Orji Administrator 7 Oct 1996 Aug 1998 Military
Abubakar Habu Hashidu Governor 29 May 1999 29 May 2003 APP
Mohammed Danjuma Goje Governor 29 May 2003 May 2011 PDP
Ibrahim Hassan Dankwambo Governor May 2011 29 May 2019 PDP
Muhammad Inuwa Yahaya Governor May 2019 Incumbent APC
Kulle

Sanannun Mutane

Wuraren ziyara a Gombe[45]

Wuraren buɗe idana a jihar sun haɗa da:[46]

  • Tomb of Sultan Attahiru
  • Gidan Sarkin Gombe.
  • Bubayero's Tomb
  • Shahararren Bima Hill
  • Tula Plateau
  • Bulok Warm Spring
  • Kalam Hill
  • Gombe National Library
  • Gombe State University Zoological Park


  • Cham Valley
  • Tsaffi burbushin Binga
  • Maƙabartar Major Mash
  • Maƙabartar LT Phillips
  • Bace Hills
  • Tula Hideout Caves
  • Kanawa Forest

Manazarta

Wikiwand in your browser!

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.

Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.