Jiha ce a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
Jihar Bayelsa jiha ce dake kudu maso kudancin Najeriya, tana nan a tsakiyar yankin Niger Delta.[1][2] An kirkiri Jihar Bayelsa[3] ne a shekarar alif dubu daya dari Tara da casa'in da shida (1996), kuma an cire ta ne daga Jihar Rivers.[4] Hakan yasa ta zamo daya daga cikin sabbin jihohin kasar. Ta hada iyaka da Jihar Rivers[5] daga gabas, da kuma Jihar Delta daga yamma, inda Tekun Atalanta[6] ta mamaye yankin kudancin jihar.[2]
Bayelsa | |||||
---|---|---|---|---|---|
Bayelsa State (en) | |||||
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Yenagoa | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 2,277,961 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 107.91 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 21,110 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar rivers | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1996 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Executive Council of Bayelsa State (en) | ||||
Gangar majalisa | Bayelsa State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-BY |
Jihar Bayelsa nada fadin fili na kimanin kilomita 10,773kmaq, wanda yasa ta zamo jiha mafi karancin fili a Najeriya.[7] Kuma tana da yawan jama’a kimanin mutum 2,394,725, (kiyasin shekara ta 2016), wanda ya sanya ta jiha mai mafi karancin mutane. Babban birnin jihar, itace Yenagoa. Douye Diri ne gwamnan jihar a shekara ta 2022, mataimakin shi kuma shine Lawrence Ewhrudjakpo.[8] Dattijan jihar sun hada da: Goodluck Jonathan, David Clark, Ben Murray Bruce, Emmanuel Paulker Izibefien da Evan Foster Ogola. A sanadiyyar kasancewarta a yankin Niger Delta, Jihar Bayelsa mamaye take da kogi da koramu, kuma kusan duka garin cikin ruwa yake, hakan ya jawo rashin cigabanta ta hanyar gina hanyoyi.[9]
Ana amfani da harshen Ijaw a ko ina a jihar, tare da sauran harsuna kamar Isoko da Urhobo a tsaffin kyaukan jihar.
Tana da kanan hukumomi 8: Ekeremor, Kolokuma/Opokuma, Yenagoa, Nembe, Ogbia, Sagbama, hi Brass da kuma Ijaw kudu. Bayelsa ta kasance gida ga Mutanen Urhobo a karamar hukumar Sagbama.[10]
A dalilin kasancewarta a yanki mai arzikin man-fetur wato Niger Delta, tattalin arzikin Jihar Bayelsa sun ta'allaka ne akan haka man-fetur da ma'aikatun tace su. Yankin Oloibiri Oilfield inda aka fara hako man fetur a Najeriya.[11] Sannan zuwa shekara ta 2015, an kiyasta cewa tana samar da kusan kashi 30-40% na man fetur din Najeriya.[12] Ana yiwa jihar lakabi da “Glory of all Lands” sannan ita ke da tafkin gas mafi girma a Najeriya (18 trillion cubic feet).[13] Duk da cewa jihar ta mallaki manyan rijiyoyin mai kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen cigaban tattalin arzikin kasa, talauci yayi wa jihar katutu, hadi da gurbacewar muhalli[14] daga fesowar man fetur.[15][16]
I' zuwa shekarar 2020, zuwa shekara ta 2023, Douye Diri ne gwamnan jihar, a yayinda Lawrence Ewhrudjakpo ke matsayin mataimakinshi.[17]
Jihar Bayelsa nada Kananan hukumomi guda takwas, Sune:
Bayelsa na daga cikin jihohin kudancin Najeriya, jihar na nan a tsakiyar yanki Niger Delta. An cire Jihar Bayelsa daga Jihar Rivers, kuma tana daga cikin sabbin jihohin Najeriya.[18]
Jihar Bayelsa ta hada iyaka da Jihar Rivers daga gabas, Jihar Delta (jiha) daga yamma, a yayin da ruwan Tekun Atalanta ya mamaye yankin kudancin Jihar.[19]
A karni na 20th, bukata na samar da sabuwar jiha da harshen Ijaw ke da rinjaye a yankin Niger Delta ya zamo sanannen abu. A tsakanin shekara ta 1941, zuwa ta 1956, an kafa kungiyoyi da dama dake goyon bayan samar da jiha na Mutanen Ijaw a yankin Kudancin Najeriya. Isaac Adaka Boro, wani shahararren dan gwagwarmayar Ijaw a shekara ta 1960, wanda aka haifa a Oloibiri yayi yinkurin ikirarin "Jimhoriyar Mutanen Niger Delta ("Niger Delta Peoples Republic") a shekara ta 1966.[20][21][22] Shugaban kasa na mulkin mallaka ya Sani Abacha ne ya kirkiri Jihar Bayelsa daga Jihar Rivers a ranar 1, ga watan Oktoban, shekara ta 1966.[23] An samo asalin sunan ne daga haruffan farko na sunayen kananan hukumomin ta: Brass LGA (BALGA), Yenagoa LGA (YELGA) da kuma Sagbama LGA (SALGA).[19]
A ranar 20, ga watan Disamban shekara ta 1999, ne sojojin Najeriya suka kaddamar da abinda aka fi sani da Kisan Kiyashin Odi. Ana kokanta akan ainihin yawan mutanen da aka kashe, duk da cewa, Nnimmo Bassey, Babban Darekta na Hakkin Harkokin Muhalli, ya sanar cewa farar hula mutum 2500, ne suka rasa rayukansu.[24][25]
Dangane da zaizayar kasa a jihar a dalilin ma'aikatun man fetur, anyi zanga-zanga da dama kamar "Rise for Bayelsa" da akayi don inganta samar da ruwan sha a kananan yankuna. A cikin shekara ta 2019, ne, gwamnatin jihar Bayelsa ta fara neman gwagwarmayar samar da mafita dangane da matsalolin gurbacewar muhalli a jihar.[26][27]
Jihar na daya daga cikin jiha mafi albarkatun man fetur a Najeriya.[28][29] A dalilin haka, akwai yawaitar man fetur a jihar. Duk da cewa jihar tana da arziki mai, jihar na samun karancin kudi daga kasafin man fetur a dalilin rashin daidaituwa a tsarin kasafi daga gwamnatin kasar.[30]
Bayelsa na zagaye da ruwan kogi da kuma koramu. Yankunan jihar da dama suna kewaye ne da ruwa wanda haka yasa ba iya riskar su ta tituna. Akwai gandun daji na "Edumanom Forest Reserve" a jihar. Tun watan Yunin shekara ta 2008, inda aka ga birin chimpanzee na karshe itace Niger Delta.[31] Sauran muhimman birane bayan Yenagoa sun hada da; Akassa, Lobia, Amassoma (the home of the Niger Delta University), Eniwari, Ekeremor, Aliebiri, Peretoru, Twon-Brass, Egwema-Brass, Kaiama, Nembe, Odi, Ogbia, Okpoama, Brass, Oporoma, Korokorosei, Otuan, Koroama, Okolobiri, Obunagha, Ogboloma, Sagbama, Olugbobiri, Peremabiri, Ekowe, da kuma Swali.
Akwai kuma ginin Akassa Lighthouse wanda ke nan tun shekara ta 1910.[32]
Asalin harshen da ake amfani dashi shine harshen Ijaw, tare da yaruka kaman Kolukuma, Mein, Bomu, Nembe, Epie-Atisa, da kuma Ogbia. Kamar dai a sauran jihohin Najeriya, Turanci ne harshen gwamnatin jihar.
Jerin harsunan Jihar Bayelsa dangane da kananan hukumomin LGA da ake amfani dasu:[33]
LGA | Languages |
---|---|
Brass | Abureni; Southeast Ijo; Ogbia; Kugbo |
Ekeremor | Izon |
Kolokuma Opokuma | Izon |
Nembe | Abureni; Southeast Ijo. Izon (Ijaw) |
Ogbia | Abureni; Southeast Ijo; Odual; Ogbia; Oruma |
Sagbama | Biseni; Isoko; Izon; Ogbah; Okodia; Urhobo |
Ijaw ta Kudu | Southeast Ijo; Izon |
Yenagoa | Engenni; Epie; Izon; Ekpeye |
Wannan wani bakin hayaki ne da ke tashi a dalilin kona man fetur ba tare da ka'ida ba (ana kiransu a gargajiyance "wutan Kpo).[34] Wadannan mugayen sinadirai kan jawo rashin lafiya kamar Ciwon huhu na daji, matsalolin fata, matsala ta mashakar iska da dai sauransu. Ana iya ganin sauran illolinta kamar gurbacewar iska, ruwa da kasa wanda hakan sun jawo mutuwan tsirrrai, mutane da kuma dabbobi.[35]
Wannan sanannen matsala ne a Jihar Bayelsa saboda tana kan gabar Tekun Atalanta. Hauhawar igiyar ruwan teku ne muhimmin dalili na ambaliyar. Ambaliyar ta haifar da matsaloli ga al'ummomi da dama, dukiyoyi da kuma mutane. Kusan ko ina a Bayelsa na fuskantar matsalolin ambaliya, amma ambaliyar tafi tasiri a yankuna kamar Ekeremor, Ijaw ta kudu, Sagbama, Kolokuma/Opokuma da kuma Yenagoa wanda suke fuskantar barazanar duk shekara.[36] Rashin bin tsarin gine-gine na daga cikin dalilan dake assasa ambaliyar a Jihar Bayelsa.[37]
Wannan wani muhimmin al'amari ne dake kawo matsalar muhalli a Jihar Bayelsa a dalilin ayyukan kamfanonin man fetur a jihar. Zubewar mai na jawo illa ga gonaki, halittun ruwa da kuma mutane.[38] Kusan duk rana ana sanarwa Udengs Eradiri labarin zubar mai a Jihar Bayelsa, Niger Delta.
Kamar yadda yake fadi, a da zaka iya yin noma ka samu girbi mai kyau, ko kuma kaje kamun kifi ka kamo da yawa, amma yanzu zaka iya kwashe tsawon yini baka kama kifi ko guda daya ba.[39]
Wata matsala ta muhalli itace gurbacewar iska (Soot), wanda mafi akasarin mutanen Bayelsa na kukan cewa basu iya numfashi da kyau.[40]
Amma a shekara ta 2018, masu hannu da shuni sunyi kamfe mai taken "Save Rivers from this soot of death" wato a kiyaye koguna daga mutuwar Soot, a yankunan dake kewaye da ruwa.[41]
Jihar Bayelsa nada makarantu mataki daban daban wanda ke bayar da ilimi ga daukacin al'ummar jihar
Makarantun gaba da sakandare a bayelsa sun hada da
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.