Harshen Karai-Karai
Harshe a Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Karai-Karai (Ajami: كاراي-كاراي) daya ne daga harsunan al'ummun Najeriya wanda ke cikin rukunin iyalan harsunan Afroasiatic. Jihohin da aka fi yawan magana da shi sun hada da jihohin Bauchi, Borno, Yobe, Gombe da sauransu. Mafi yawan wuraren da aka fi samun al'ummar da ke magana da wannan harshe akasari suna zaune ne a garuruwan da suke cikin yankin da ake kira Ƙasar Karai-Karai ko Daular Karai-Karai wanda ya kasance gurbin wurin da ke tsakanin yammacin tsohuwar Daular Borno da kuma gabashin Kasar Hausa wanda Kuma a yanzu ya kuma shafi garuruwan da a cikin su suka hada da Kukar-Gadu, Dagare, Maje, Potiskum, Fika, Nangere, Dambam, Kalam, Jalam, Gulani, Daya, Damagum, Gujba, Ngelzarma, Deba, Janda da kuma Misau duk a cikin Najeriya. Daga cikin ire-iren karin harshen akwai Birkai, Jalalum, Ngwajum, da kuma Pakarau. [2][3][4]
Harshen Karai-Karai | |
---|---|
'Yan asalin magana | 1,800,000 |
| |
Baƙaƙen rubutu | Baƙaƙen boko |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-3 |
kai |
Glottolog |
kare1348 [1] |