Karamar hukuma a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
Nangere karamar hukuma ce dake jihar Yobe a Najeriya. Hedkwatarta na nan a garin Sabon Gari Nangere (ko Sabon Garin) a kan hanyar zuwa Gashua daga Potiskum a11°51′50″N 11°04′11″E.
Nangere | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Jihar Yobe | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 980 km² |
Karamar hukumar Nangere tana da girman kilomita murabba'i 980 kuma tana da matsakaicin yanayi na zafi/sanyi na 34 °C. Karamar hukumar ta nada manyan yanayi guda biyu da suka hada da rani da damina yayin da aka kiyasta yawan ruwan sama a yankin ya kai milimita 890 na ruwan sama a shekara.[1]
Garin na da jimillar yawan jama'a 87,823 a Kidayar 2006.
Nangare na da lambar akwatin gidan waya na yankin ita ce 631.[2]
Sauran garuruwa da kauyukan da suka hada da karamar hukumar Nangere sun hada da Dawasa, Tagamasa, Sabon Gari Nangere, Tikau, da Dorowa.
Yawancin mazauna Nangere suna gudanar da ayyukan noma. Ana noman amfanin gona iri-iri a karamar hukumar yayin da ake kiwon dabbobi da sayar da su a yankin. Har ila yau ciniki ya bunkasa a karamar hukumar Nangere inda yankin ke da kasuwanni da dama inda ake saye da sayar da kayayyaki iri-iri. Sauran muhimman ayyukan tattalin arziki da jama'ar karamar hukumar Nangere ke gudanarwa sun hada da farauta, sana'ar fata da sana'o'in hannu da sauran su.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.