Yobe
Jiha a arewa maso gabashin Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Arewacin Najeriya Yobe jiha ce daga cikin jerin jihohin shiyyar Arewa[1] Maso Gabashin Najeriya.[2] [3]Tana da yawan ƙasa kimanin murabba'in kilomita 45,502 da yawan jama’a miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu da sha- ɗaya da ɗari huɗu da tamanin da ɗaya "1,411,481" (a ƙidayar yawan jama'a ta shekarar 1991).[4] [2]Babban birnin jihar shi ne Damaturu. Mai Mala Buni[5] shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta 2015 zuwa yau[6]. Mataimakin[7] gwamnan shi ne Idi Barde Gubana[8].Jihar dai tana da bangarori guda uku: bangaren gabas, kudu da kuma arewa[7]. 'yan majalisar Dattijan jihar su ne: Ahmed Ibrahim Lawan[9] mai wakiltar shiyyar arewaci, Bukar Abba Ibrahim Ibrahim Gaidam[10] shiyyar gabashi da, Ibrahim Mohammed Bomai shiyyar kudanci.
Yobe | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Suna saboda | Komadugu Yobe | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Damaturu | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,294,137 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 72.4 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 45,502 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Komadugu Yobe | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Borno | ||||
Ƙirƙira | 27 ga Augusta, 1991 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | executive council of Yobe State (en) | ||||
Gangar majalisa | Majalisar dokokin Jihar Yobe | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-YO | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | yobestate.gov.ng |
Jihar Yobe tana da iyaka da jihohi huɗu, Kamar haka: Bauchi, Borno, Gombe da kuma Jigawa. Tana kuma da iyaka da jamhuriyar Nijar.[3]