Daniel Etim Effiong

Dan wasan kwaikwayo, mai rubuta fim, kuma darakta. From Wikipedia, the free encyclopedia

Daniel Etim Effiong

Daniel Etim Effiong, kuma Daniel Etim-Effiong[1] ɗan wasan Nollywood ne na Najeriya kuma darektan fina-finai.[2]

Quick Facts Rayuwa, Haihuwa ...
Daniel Etim Effiong
Thumb
Rayuwa
Haihuwa Jahar Kaduna, 
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Federal University of Technology, Minna Digiri a kimiyya : chemical engineering (en)
Jami'ar Johannesburg
Matakin karatu Digiri
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a jarumi, darakta, chemical engineer (en) da marubin wasannin kwaykwayo
IMDb nm5652097
Kulle
Thumb
Daniel Etim Effiong

Rayuwa da ilimi

An haife shi a Jaji, jihar Kaduna a Najeriya kuma ya rayu a birnin Benin na jihar Edo ; Jihar Legas da Abuja. Mahaifinsa yana cikin sojojin Najeriya.[3] Mahaifinsa, Laftanar Kanar Moses Effiong ya samu afuwa a hukumance daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu mutane biyar da aka yankewa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a shekarar 1986, bayan da aka zarge shi da yin juyin mulki na mai taken, 'Vatsa' a lokacin mulkin Ibrahim Babangida, bisa zarginsa da laifin ɓoyewa gwamnatin ƙasar da cin amanar ƙasa, wanda aka saki a shekarar 1993 amma ba tare da shela a hukumance da maido masa da muƙamin sa da hakki ba.[4]

Thumb
Daniel Etim Effiong

Ya halarci makarantar St. Mary's Private School, Legas Island, Legas sannan ya ci gaba da karatunsa na sakandare a Kwalejin Gwamnati, Ikorodu, Legas. Daga nan sai ya wuce Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna ta Jihar Neja, inda ya yi karatun digiri na farko a fannin injiniyan sinadarai. Bayan wani ɗan takaitaccen lokaci na aiki a masana’antar man fetur da iskar gas a matsayin injiniya, ya yanke shawarar sauya sana’a sannan ya ci gaba da karatun harkar fim, rubutu da bayar da umarni a Makarantar Fina-Finai ta AFDA da ke kasar Afirka ta Kudu sannan ya yi kwas a Jami'ar Johannesburg kan shirya fina-finai.[3]

Sana'a

Bayan ya bar aikin mai da iskar gas, ya zama mai shirya wasu tsare-tsare ga NdaniTV.[5]

A cikin 2017, ya shirya wani gajeren fim mai tsawon minti biyar mai suna, " Prey ", wanda amaryarsa, Toyosi ta shirya, tare da Tope Tedela da kuma Odenike Odetola.[6]

Bland2Glam ta nuna shi a cikin 2019 a lokacin kamfen ɗinta na #ThePowerof7 don bikin shekara bakwai a masana'antar, fashion industry.[7]

Ya fito tare da 'yan wasan kwaikwayo na Kenya Sarah Hassan da Catherine Kamau Karanja a cikin fim ɗin barkwanci na shekarar 2019, mai suna Plan B inda ya taka rawar a matsayin Dele Coker, shugaban Najeriya na wani kamfani da ke Nairobi.[8][9][10][11] A dalilin Fim ɗin ya sami lambar yabo ta Mafi kyawun ɗan wasan kwaikwayo a cikin shirin barkwanci (Fim / TV Series) a cikin jerin lambobin yabon da aka bayar na AMVCA karo na 7, da aka bayar a shekarar 2020.[5]

Ya fito a cikin fina-finai da yawa da akayi a shekara ta 2020. Ya taka rawar gani a fim din " Fish Bone ", wanda Editi Effiong ya shirya shi ma Shaffy Bello da Moshood Fattah.[12] An nuna shi tare da Ike Onyema da Atteh 'SirDee' Daniel a cikin gajeren fim ɗin, " Storm ", wanda Diane Russet ya shirya kuma Michael 'AMA Psalmist' Akinrogunde ya ba da umarni.[13][14] Har yanzu a cikin 2020, ya ba da umarnin wani shirin gaskiya mai taken, " Skin ", wanda Beverly Naya ya shirya.[15][16] An tsara shi don nunawa akan dandalin kallo a yanar gizo wato NETFLIX.[17]

Filmography

Shirye-shiryen TV

Ƙarin bayanai Shekara, Suna ...
Shekara Suna Matsayi Bayani Madogara
2019 Castle and Castle Mike Amenechi [18]
2018- The Men’s Club Lanre [19]
2013 Gidi Up Folarin [19]
2021 Castle & Castle Mike Amenechi [20]
2022 Blood Sisters
Kulle

Fina-finai

Ƙarin bayanai Shekara, Suna ...
ShekaraSunaMatsayiBayani Madogara
2022 Kofa Wale Earned AFRIFF award and AMVCA nomination [21]
2021Still FallingCaptain Lagi Alongside Sharon Ooja [22]
2020SkinDirector Documentary Featuring Eku Edewor and Beverly Naya [23]
2020StormStorm Short film alongside Diane Russet [24]
2020Fish BoneInspector Shortfilm alongside Shafy Bello and Moshood Fattah [25]
2019ÒlòtūréTony [26]
2019 Makate Must Sell
2019Plan BDele CokerLead role [27]
2018New MoneyGaniyu Osamede [28]
2017PreyDirector Short skit [25]
Kulle

Kyaututtuka da zaɓe

Ƙarin bayanai Shekara, Kyauta ...
Shekara Kyauta Iri Fim Sakamako Madogara
2022 Africa International Film Festival Best Actor In A Drama, Movie Or TV Series Kofa Lashewa [21]
2023 Africa Magic Viewers' Choice Awards Best Actor In A Comedy Drama, Movie Or TV Series Ayyanawa [29][30]
Kulle

Rayuwa ta sirri

Effiong ya auri Toyosi Etim-Effiong tun ranar 4 ga Nuwamba, 2017. Sun fara arba-(haduwa) ne a watan Agustan 2016 yayin gudanar da wani aiki.[31][32] Ma'auratan sun yi maraba da ɗansu na fari, mace a watan Janairu 2019.[33]

Manazarta

Hanyoyin haɗi na waje

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.