Ban Ki-moon
From Wikipedia, the free encyclopedia
Ban Ki-moon (Haihuwa 13 Yunin shekarar 1944) dan siyasa na na kasar South Korea kuma ma'aikacin harkokin kasa da kasa wanda yayi aiki a matsayin Babban Sakatare na majalisar dinkin duniya na 8, daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2016. Kafin ya zamo babban sakatare na majalisar dinkin duniya, Ban Ki-Moon ya kasance dan demukradiya na Ma'aikatar Harkokin Waje na Korea ta Kudu da kuma Majalisar Dinkin Duniya. Ya shiga harkar siyasa na kasa da kasa ne bayan kammala karatun sa na jami'a inda ya fara aikinsa na farko a New Delhi, Indiya.
Ban Ki-moon | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Murya | |||||||||
Satumba 2017 -
1 ga Janairu, 2007 - 1 ga Janairu, 2017 ← Kofi Annan - António Guterres →
17 ga Janairu, 2004 - 10 Nuwamba, 2006 ← Yoon Young-kwan (en) - Song Minsoon (en) →
| |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Eumseong County (en) , 13 ga Yuni, 1944 (80 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Koriya ta Kudu | ||||||||
Mazauni |
North Chungcheong (en) New York | ||||||||
Harshen uwa | Korean (en) | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta |
Seoul National University (en) Chungju High School (en) John F. Kennedy School of Government (en) Jami'ar Harvard | ||||||||
Harsuna |
Turanci Korean (en) Faransanci | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa, Mai wanzar da zaman lafiya da marubuci | ||||||||
Employers | Majalisar Ɗinkin Duniya (1 ga Janairu, 2007 - 1 ga Janairu, 2017) | ||||||||
Kyaututtuka |
gani
| ||||||||
Mamba | ABLF alumni network (en) | ||||||||
Imani | |||||||||
Addini |
Konfushiyanci Buddha | ||||||||
Jam'iyar siyasa | independent politician (en) | ||||||||
IMDb | nm2559634 | ||||||||
Ban ya kasance minista na harkokin kasashen waje na Korea ta Kudu a tsakanin shekara ta 2004 zuwa 2006. A cikin watan Febrerun 2006 ne, Ban ya fara takarar kujerar babban sakatare a majalisar dinkin duniya. An dauki Ban a matsayin wadda bai dace da kujerar ba a farkon lamari. Amma a matsayin sa na ministan harkokin kasahen waje na Korea ta Kudu, Ban yayi amfani da wannan dama ya zagaye duka kasashen dake karkashin majalisar dinkin duniya, hakan ya masa amfani a siyasance.
A ranar 13 ga watan Oktoban shekara ta 2006 ne, Majalisar Dinkin Duniya ta zabi Moon a matsayin babban sakatare na kungiyar.A ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2007 ne, Moon ya amshi ragamar mulkin daga hannun Kofi Annan. A matsayin sa na babban sakatare na majalisar, ya dauki ragamar ayyuka da dama ta fannin zaman lafiya da kuma daukan ma'aikata daga sassa daban daban na duniya. A siyasance, Ban ya dauki tsatstsaurar ra'ayi akan harkar dumamar yanayi inda yayi ta zantawa da shugaban kasan Amurka, George W Bush, da kuma Rikicin Darfur, inda ya taimaka wajen janyo hankalin shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir da ya bar sojojin kwantar da tarzoma na Majilasar Dinkin Duniya su shiga Kasar.[1][2]
An sanya Ban na 32 a cikin jerin shahararrun mutanen duniya a jerin sunaye na Forbes a shekara ta 2013. Sannan shine na farko a cikin jerin mutanen Koriya ta Kudu.[3]A cikin shekara ta 2014 ne aka sanya shi na uku daga cikin shahararrun mutanen Koriya ta Kudu, a bayan Lee Kun-hee da Lee Jae-yong.[4] A cikin shekara ta 2016 ne, Mujallar Foreign Policy ta sanya Ban acikin jerin masu Zurfin Tunani na Mutum 100 na Duniya, bayan ya taimaka wajen kaddamar da Yarjejeniyar Parisa da kuma tabbatar da ta fara aiki acikin kankanin lokaci na kasa da shekara daya bayan kaddamar da ita.[5]