Ali Bongo Ondimba
Shugaban kasar Gabon / From Wikipedia, the free encyclopedia
Ali Bongo Ondimba (an haife shi Alain Bernard Bongo ; 9 ga watan Fabrairu shekarar 1959), [1] wani lokaci ana kiransa Ali Bongo, ɗan siyasan, Gabon ne wanda shine shugaban Gabon na uku daga shekarar 2009 zuwa shekara ta 2023. [2] Dan jam'iyyar Democradiyyar Gabon ne .
Ali Bongo Ondimba | |||||
---|---|---|---|---|---|
16 Oktoba 2009 - 30 ga Augusta, 2023 ← Rose Francine Rogombe (en) - Brice Oligui Nguema (en) →
1989 - 1991 ← Martin Bongo (en) - Pascaline Bongo Ondimba (en) → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Brazzaville, 9 ga Faburairu, 1959 (65 shekaru) | ||||
ƙasa | Gabon | ||||
Ƴan uwa | |||||
Mahaifi | Omar Bongo | ||||
Mahaifiya | Patience Dabany | ||||
Abokiyar zama |
Sylvia Bongo Ondimba (en) (1989 - Inge Lynn Collins Bongo (en) (1994 - 2015) | ||||
Yara | |||||
Ƴan uwa |
view
| ||||
Karatu | |||||
Makaranta | University of Paris 1 Pantheon-Sorbonne (en) | ||||
Harsuna |
Faransanci Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya, ɗan siyasa da Lauya | ||||
Mahalarcin
| |||||
Kyaututtuka | |||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa | Gabonese Democratic Party (en) | ||||
presidentalibongo.com |
Ali Bongo dan Omar Bongo ne, wanda ya kasance shugaban kasar Gabon daga 1967 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2009. A lokacin shugabancin mahaifinsa, ya kasance Ministan Harkokin Waje daga 1989 zuwa 1991, ya wakilci Bongoville a matsayin mataimaki a Majalisar Dokoki ta kasa daga 1991 zuwa 1999, kuma ya kasance Ministan Tsaro daga 1999 zuwa 2009. Bayan rasuwar mahaifinsa, ya lashe zaben shugaban kasar Gabon a shekara ta 2009 . [3] An sake zabe shi a shekara ta 2016, a zabukan da suka yi fama da kura-kurai da dama da tsare mutane da take hakkin dan Adam da zanga-zangar bayan zabe da tashin hankali . [4] Sojoji sun tumbuke shi daga shugabancin kasar bayan sakamakon zaben gama gari na Gabon na 2023, a juyin mulkin da aka yi a Gabon a 2023 .