Yahaya Bello
Dan siyasan Nigeria / From Wikipedia, the free encyclopedia
Yahaya Adoza Bello ɗan kasuwa ne kuma dan siyasa ne a Najeriya wanda shine wamnan Jihar Kogi tun a shekara tYa 2016.[1] ɗan jam'iyyar APC, Yahaya Bello ya kasance gwamna mafi ƙarancin shekaru a Najeriya. An haife shi a Okene, Bello ya kasanci ya Karanci Kwos din Accounting da fannin kasuwanci a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, jihar Kaduna. kafin ya fara aiki a tsakiyar shekarun 2000. Zaɓen sa ya fara ne da rashin nasara a hannun Abubakar Audu a zaɓen fidda gwanin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a shekarar 2015 kafin Audu ya lashe babban zaɓe; sai dai Audu ya rasu ranar zabe aka zaɓi Bello a matsayin wanda zai maye gurbinsa a matsayin dan takarar jam’iyyar kuma aka rantsar da shi a shekara mai zuwa.[2] Bayan shekaru hudu, an sake zaɓensa a matsayin gwamnan Kogi. Duk da cewa ana samun rahotannin tashin hankali da zamba.[3][4] Bayanansa ya tashi cikin sauri a tsawon wa'adinsa, wani bangare na kuruciyar sa idan aka kwatanta da sauran ’yan siyasar Najeriya tare da maganganunsa masu cike da cece-kuce da kuma kudaden da ake tambaya. [5]
![]() | |||
---|---|---|---|
![]() | |||
27 ga Janairu, 2016 - ← Idris Wada | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Yahaya Adoza Bello | ||
Haihuwa | Okene, 18 ga Yuni, 1975 (49 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Amina Oyiza Bello | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da ɗan kasuwa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/7/73/Bolori.jpg/640px-Bolori.jpg)