Umar Ibn Al-Khattab
From Wikipedia, the free encyclopedia
Umar, ko kuma a Turanci Omar a Larabci kuma عمربن الخطاب Umar dan Al'Khattab hausa Umaru dan Kaddabi Allah ya kara yarda da shi.
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Umar Ibn Al-Khattab | |||
---|---|---|---|
22 ga Augusta, 634 - 3 Nuwamba, 644 ← Sayyadina Abubakar - Sayyadina Usman dan Affan → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Makkah, 586 | ||
ƙasa | Khulafa'hur-Rashidun | ||
Mutuwa | Madinah, 3 Nuwamba, 644 | ||
Makwanci | Masallacin Annabi | ||
Yanayin mutuwa | kisan kai (stab wound (en) ) | ||
Killed by | Abu Lu'lu'a (en) | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Al-Khattab bin Nufayl | ||
Mahaifiya | Ḥantamah bint Hishām | ||
Abokiyar zama |
Ummu Kulthum bint Ali Umm Kulthum bint Jarwal (en) Quraiba bint Abi Umayya Umm Kulthum bint Asim (en) Atika bint Zayd (en) Zaynab bint Madhun (en) | ||
Yara |
view
| ||
Ahali | Zayd ibn al-Khattab (en) da Fatimah bint al-Khattab (en) | ||
Ƴan uwa |
view
| ||
Karatu | |||
Harsuna | Larabci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | statesperson (en) , Caliph (en) , Liman, shugaban addini da Sahabi | ||
Aikin soja | |||
Ya faɗaci |
Badar Yaƙin Uhudu Yaƙin gwalalo Yaƙin Khaybar | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Ɗaya ne daga cikin manyan Sahabban Annabi Muhammad (s.a.w), Wanda ake wa laƙabi da suna Faruk (wato me rarrabe Ƙarya da Gaskiya), kuma shine na biyu cikin halifofin Musulunci. Yana ɗaya daga cikin Halifofinnan guda huɗu na Halifancin Annabta, sannan kuma yana ɗaya daga cikin sahabbai goman da Annabi yayima bushara da Aljanna tun suna Duniya. Umar ya kasance mai taka tsan-tsan tare da gudun duniya, kasancewar sa mutumin da yayi kaurin suna kwarai wajen rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ne yasa akayi masa laƙabi da Al'faruk, ma'ana mai raba ƙarya da gaskiya. Umar ya kasance babban jagora, kuma dukkannin hadisan ruwayar shi ana kallonsu a matsayin hadisai ingantattu.