Muhammad Yusuf
From Wikipedia, the free encyclopedia
Muhammad Yusuf Ya kasance kuma an Haife shi a ranar: 29 ga watan Janairun Shekara ta 1970 - ya Mutu a ranar: 30 ga watan Yulin shekara ta 2009), kuma an san shi da Ustaz Mohammad Yusuf, dan Nijeriya ne kuma malamin addinin musulunci ne. wanda ya kafa akidar cewa karatun boko haramun ne, an masa kallan dan ta'adda wanda ya kafa kungiyar Boko Haram a Najeriya a shekara ta 2002, wanda yanzu haka tasirin wannan gungiyar ta Boko Haram ya shiga kasar Nijar, Cadi, da Kamaru, Shi ne shugaban ta na farko har aka kashe shi a rikicin Boko Haram na farko a cikin garin Maiduguri [1], wanda daga baya mataimakin sa Abubakar Shekau ya ci gaba da jagoranta. Muhammad yusuf ya kasance yana bibiyan karatun Mallam Ja'afar Mahmud Adam wanda mallam Ja'afar ya hadu da shi a makkah ya nuna masa wannan akida da yake so ya kafa mutane a kai ba daidai ba ne ya rantse da Allah cewar wadannan mutanan ba dalibansa ba ne ya kara da cewa shi bai san su ba sai mallam ja'afar mahmud adam ya ce indai kana son ka kubuta daga wannan aqida to ka dauki alkalin da zai rubuta da yawunka kai ka kubuta daga wannan aqida da ake jingina ka da ita haka muhammad yusuf ya sa aka samo alkalin da suke cewa aikin boko haramun ne shine yayi masa rubutu da yaran da ake cewa haramun ne akayi har ,muhammad yusuf yasamu yadawo najeriya daga baya ya nuna wa duniya shi yana nan akan bakan sa na nunawa duniya cewa yin karatun boko haramun ne.
![]() |
![]() ![]() |
![]() | |||
---|---|---|---|
2002 - 30 ga Yuli, 2009 - Abubakar Shekau → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jihar Yobe, 29 ga Janairu, 1970 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | Maiduguri, 30 ga Yuli, 2009 | ||
Yanayin mutuwa |
(extra-judicial killing (en) ![]() | ||
Ƴan uwa | |||
Yara |
view
| ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai da'awa | ||
Aikin soja | |||
Ya faɗaci | Rikicin Boko Haram | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |