Hissène Habré
From Wikipedia, the free encyclopedia
Hissène Habré ( Larabci : حسين حبري Ḥusaīn īabrī , Larabcin Chadi : pronounced [hiˈsɛn ˈhabre] ; French pronunciation: [isɛn abʁe] . an haife shi ranar 13 ga watan Agusta na shekarar 1942), har wayau akan rubuta sunansa da Hissen Habré, tsohon dan siyasar Chadi ne wanda ya yi Shugabancin Chadi daga shekarar 1982 har zuwa lokacin da aka sauke shi a shekarata 1990. An kawo shi kan mulki ne tare da goyon bayan Faransa da Amurka, wadanda suka ba da horo, makamai, da kuma kudade.
Hissène Habré | |||||
---|---|---|---|---|---|
7 ga Yuni, 1982 - 1 Disamba 1990 ← Goukouni Oueddei (en) - Idriss Déby →
29 ga Augusta, 1978 - 23 ga Maris, 1979 ← Ngarta Tombalbaye - Djidingar Dono Ngardoum (en) → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Faya-Largeau (en) , 13 ga Augusta, 1942 | ||||
ƙasa | Cadi | ||||
Mutuwa | Dakar, 24 ga Augusta, 2021 | ||||
Makwanci | Yoff (en) | ||||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Koronavirus 2019) | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Sciences Po (en) Makarantar mulkin mallaka, Paris Aosta Valley University (en) | ||||
Harsuna |
Faransanci Larabci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||||
Kyaututtuka | |||||
Aikin soja | |||||
Fannin soja |
People's Armed Forces (Chad) (en) Armed Forces of the North (en) | ||||
Ya faɗaci |
Chadian–Libyan War (en) Toyota War (en) Chadian Civil War of 1965–1979 (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa |
FROLINAT (en) National Union for Independence and Revolution (en) Armed Forces of the North (en) |
A watan Mayun shekarata 2016, wata kotun kasa da kasa da ke Senegal ta same shi da laifin cin zarafin dan Adam, ciki har da fyade, bautar da mata don jima’i, da ba da umarnin kashe mutane 40,000, sannan aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Shine tsohon shugaban kasa na farko da aka yankewa hukunci saboda take hakkin dan adam a kotun wata kasa.