From Wikipedia, the free encyclopedia
Vice Admiral Joseph Edet Wey (ya rayu daga Mayu 6, 1918 zuwa Disamba 12, 1991)[1] ya kasance hafsan sojin Ruwa ne a Nijeriya, yayi aiki a lokuta daban-daban, a matsayin sa na shugaban Nigerian Navy (wato Chief of Naval Staff),[2] da kuma Ministan Harkokin waje na wucin gadi,[3] sannan kuma ya zama Chief of Staff na Supreme Headquarters,[4] haka yasa ya zama de facto Mataimakin Shugaban Nijeriya lokacin janar Yakubu Gowon.
Joseph Edet Akinwale Wey | |||||
---|---|---|---|---|---|
29 ga Yuli, 1966 - 29 ga Yuli, 1975 ← Babafemi Ogundipe (en) - Olusegun Obasanjo →
1964 - 1973 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | ga Maris, 1918 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Yarbawa | ||||
Mutuwa | 12 Disamba 1990 | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Ibibio Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Digiri | admiral (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Kiristanci |
An haife shi a birnin Calabar a watan Maris shekarar 1918 a gidan Yarbawa da Ibibiyo/Efik wato mahaifinsa da mahaifiyar sa, Admiral Wey yayi karatunsa na farko a Calabar, Cross River State makarantar firamare na Methodist, Ikot Ekpene a Jihar Akwa Ibom a yanzu; sannan ya cigaba da karatunsa a Jihar Lagos. Ya fara aikin sa na farko a Marine Department a matsayin cadet kuma mai koyon zama injiya a 1940. A karshen koyon aikin sa a 1945, yayi aiki a dukkanin sea-going vessels dake a Marine Department. Lokacin da aka kirkiri Nigerian Navy a shekarar 1956, an maida shi bangaren Navy a matsayin sub-lieutenant. A 1962, an naɗa shi hafsa mai bada umurni na base da naval officer da ke rike da yankin Apapa, Lagos. A 1966, an nada shi Federal Commissioner na Establishment kuma ya zama mamba a federal Executive Council. An masa Karin girma da dama inda ya kai har zuwa matsayin vice-admiral.
mukaman da ya rike a soja sune:
Yayi ritaya a 1975 bayan samun juyin mulki da ta kawo Murtala Mohammed a shugaban cin kasa [4], wacce ta maye gurbin mulkin gwamnatin janar Yakubu Gowon. Ya rasu a 12 December 1991.[1]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.