From Wikipedia, the free encyclopedia
Ike Ekweremadu (an haife shi 12 ga watan mayun, shekarar alif dari tara da sittin da biyu 1962) a kauyen Amachara Mpu da ke Karamar hukuma Aninri a Jihar Enugu.[1] Ɗan Nijeriya ne, dan siyasa kuma lauya, wanda ya kasance sanata a majalisar dattawan Nijeriya tun daga watan Mayu shekara ta 2003. Dan jam'iyar People's Democratic Party (PDP) ne, kuma shine Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa karo na uku (6th, 7th and 8th) kenan.[2][3] A ranar 23 ga Yuni 2022, an tuhumi Ekweremadu tare da matarsa a Kotun Majistare ta Burtaniya da laifin hada baki don shirya Safarar dan shekara 21 zuwa Burtaniya domin cire wani sassa a jikin sa.[4] An same shi da laifi a ranar 23 ga watan Maris 2023 a Kotun hukunta manyan laifuka ta, Old Bailey.[5]
Ike Ekweremadu | |||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
5 ga Yuni, 2007 - 9 ga Yuni, 2019 ← Ibrahim Mantu - Ovie Omo-Agege →
3 ga Yuni, 2003 - ga Yuni, 2007 ← Ben-Collins Ndu District: Enugu West
District: Enugu West
District: Enugu West
District: Enugu West
District: Enugu West | |||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||
Cikakken suna | Ike Ekweremadu | ||||||||||||
Haihuwa | Jihar Enugu, 12 Mayu 1962 (62 shekaru) | ||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||
Karatu | |||||||||||||
Makaranta |
Jami'ar Najeriya, Nsukka Jami'ar Abuja | ||||||||||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||||||
Imani | |||||||||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
An haifi Ike Ekweremadu a Amachara Mpu da ke karamar hukumar Aninri ta jihar Enugu, kuma dan kabilar Igbo ne. Ya yi digirinsa na farko da na biyu a fannin shari'a a Jami'ar Najeriya, sannan aka kira shi zuwa Nigerian Bar a 1987. Ya kuma yi digirin digirgir a fannin shari'a a Jami'ar Abuja, Najeriya.[6][7][8]
An nada shi a matsayin shugaban zartarwa na karamar hukumar Aninri a karkashin jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) a shekarar 1997 kuma ya lashe mafi kyawun shugaban majalisar na shekara, a 1997.[6][9]
A cikin watan Satumba na 2009, an nada shi shugabancin kwamitin rikon kwarya na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) don yin aikin dawo da tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar.[10] An zaɓe shi mataimakin shugaban majalisar ECOWAS na farko kuma ya zama shugaban majalisar yankin a watan Agustan 2011.[11]
A ranar 12 ga Afrilu 2003 aka zabe shi a matsayin dan majalisar dattawan Najeriya.[12] A watan Satumban 2003, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai, Cif Ekweremadu ya bayyana cewa majalisar za ta yi bincike mai zurfi kan zargin karbar cin hanci da ministan babban birnin tarayya (FCT) Mallam Nasir el-Rufai ya yi.[13] Dangantaka tsakanin Nasir El-Rufai da majalisar dattawa ta ci gaba da yin tsami, kuma daga karshe an tuhumi El-Rufai da laifin almundahana a shekarar 2008.[14][15] A shekarar 2005, Sanata Kenechukwu Nnamani ya doke Ike Ekweremadu a takarar shugaban majalisar dattawan Najeriya.[16]
An kama tsohon Sanatan da matarsa Beatrice a kasar Birtaniya kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.[17][18][19][20][21][22][23] Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za'a gurfanar da su a kotu bayan gudanar da bincike. Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da binciken ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.[24]
▶Bayan zaman kotun na farko kotun ta hana belin shi Ekweremadu da matarsa, hakan na nufi zasu cigaba da kasancewa a tsare har sai sun sake gurfana gaban kuliya a ranar 7 ga watan Yulin 2022 mai zuwa.[25]
Ranar 5 ga watan Agusta, An dage shari'ar da'ake ma Sanata Ekweremadu zuwa watan 31 ga watan Oktoba, amma sauraron ƙara da gabatar da shaidu a shari'ar sai watan Mayu na shekarar 2023 Oktoba.[26]
A ranar 23 ga watan Maris 2023 Ekweremadu, da matarsa da Dokta Obinna Obeta an same su da laifin haɗa baki wajen yin amfani da kodar mutumin. Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotun Old Bailey cewa an kawo wanda aka kashen zuwa Burtaniya a shekarar 2022 don cire kodar a cikin wani ɗaki na sirri, akan fam 80,000, a asibitin Royal Free Hospital, London. Masu gabatar da ƙara sun tabbatar da mafi ƙaranci zaman gidan yari, akan shari'ar safarar sata sassan bil'adama shi ne, hukuncin ɗaurin rai-da-rai ne.[27] Za a cire gabobin a ba wa ‘yar ma’auratan – ɗiyar ma'auratan an wanke ta daga wannan tuhume-tuhume.[28]
A watan Yulin 2018, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kasar najeria ta gayyaci shi don amsa tambayoyi kan zargin rashawa.
Ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2019, an Ike Ekweremadu ya ziyarci Nuremberg, ƙasar Jamus don halartan wani taro da suka shirya, wasu fusatattun matasa suka far masa. Jim kaɗan da faruwar hakan sai bidiyo ya bayyana soshiyal midiya inda aka ga Ekweremadu yana kokarin neman tsira da rayuwarsa a yayin harin.[29]
Sukar Peter Obi. A wani bidiyon kuma da ya bayyana shima a soshiyal midiya, anji Ekweremadu na faɗar wani yani a nigeria ba za su yarda su mara ma Peter Obi baya ba a babban zaben shugaban kasa.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.