From Wikipedia, the free encyclopedia
João Fernando Nelo (an haife shi a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 1979 a São Paulo ), wanda aka fi sani da Fernando Baiano, dan kwallon Brazil ne da ya buga wa Mogi Mirim Esporte Clube a matsayin dan wasan gaba. Sunyi aure da Bruna Lopes tun a shekara ta 2011.
Fernando Baiano | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | São Paulo, 18 ga Maris, 1979 (45 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Brazil | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 81 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 185 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sunan mahaifi | Baiano |
Bayan ya kammala shekaru biyar a ƙasar Brazil tare da Kungiyoyin kwallon kafa na gida wato Corinthians Paulista, Internacional Porto Alegre da Clube de Regatas do Flamengo, Baiano ya ƙaura zuwa ƙasashen waje, yana cikin ƙungiyar Bundesliga ta VfL Wolfsburg kuma ya saka ƙwallaye 11 a kakar wasa ɗaya, wanda daga bisani ya koma ƙasarsa izuwa kungiyar wasan kwallon kafa ta Associação Desportiva São Caetano.
A watan Janairun shekarar 2005, Baiano ya sanya hannu kan kungiyar Málaga FC ta La liga,[1] inda ya saka kwallaye 9 wanda ya taimakawa kungiyar ta Andalusia kaiwa matakin tsakiyar teburi a karshen kakar. A lokacin bazarar, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Celta de Vigo,[2] a yayin da yake wasa a Galicia, kulob din zai shiga gasar cin kofin UEFA amma kuma za a koma Segunda División, tare da dan wasan yana ba da gudummawa da kwallaye 32 a wasanni 80 da ya buga a hukumance.[3]
Dab da tafiyar Celta zuwa kananun matakan wasanni (relegation), Baiano ya amince da kwantiragin shekaru uku tare da kungiyar Real Murcia, kan kusan Yuro miliyan €5. Bayan ya saka kwallaye biyar kacal a raga a lokacin kakar 2007-08 kungiyar tasa ta kuma kare a mataki na biyu daga kasa, wanda daga bisani suka tafi relegation.[4][5]
A watan Agustan shekarar 2008 aka bai Baiano aro ga kungiyar Al Jazira Club, dake Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). A watan Yuni na shekara mai zuwa ya koma wani bangare a cikin garin, Al-Wahda SCC, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu a kan m 5million - dan wasan da farko ya nemi yarjejeniyar shekaru uku a kan € 9m.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.