From Wikipedia, the free encyclopedia
Emmanuel Ifeanyi Ikubese (an haifeshi ranar 12 ga Agusta, 1991) ɗan Najeriya kuma ɗan wasan kwaikwayo, wanda ya lashe lambar zinare da kamfanin SilverBird ke shiryawa maza, watau kyautar Mr. Nigeria a shekarar 2014.[1][2][3] A cikin 2015, ya lashe lambar yabo ta Zaman Lafiya ta Shekara[4] a lambar yabo ta Aminci Achievers kuma a cikin 2016 ya sami lambar yabo ta City People Award ta Most Promising Actor of the Year a bikin bayar da kyauta ta City People Entertainment Awards.[5][6] Ikubese, a cikin 2017 an naɗa shi jakadan United Nations Millennium Development Goals.[7][8]
Ikubese ɗan asalin jihar Delta ne a Najeriya, yanki ne da ya kunshi ƙananan kabilu a Najeriya da kuma kabilar Igbo suka mamaye. Ikubuese ya samu shaidar kammala karatunsa na farko da kuma takardar shaidar kammala sakandare ta yammacin Afirka daga cibiyoyin koyo na cikin gida a jihar Delta. A ƙoƙarinsa na samun digiri a jami'a ya yi hijira zuwa kasar Kenya inda ya nemi gurbin karatu a jami'ar United States International University Africa da ke birnin Nairobi, domin karantar huldar kasa da kasa inda a karshe ya samu karɓuwa, ya yi digirin sa na farko, biyo bayan kammala karatunsa na tsawon lokacin karatun digirin.[9]
Ikubese ya fara aikinsa ne a matsayin kwararren abin koyi-(professional model)[10] a harabar jami'ar da yayi, kuma daga karshe ya samu sarautar Mr.Nigeria sannan kuma ya kammala a matsayin wanda ya zo na ɗaya a gasar zakarun maza na Mr.World. Ikubuese bayan nasarar da ya samu a matsayin abin koyi, ya shiga masana’antar fina-finan Najeriya da aka fi sani da Nollywood kuma ya samu karɓuwa sosai bayan ya taka rawar gani a cikin shirin MTV Tv mai suna Shuga inda ya fito a matsayin wani jarumi mai suna Femi a cikin shirin fim ɗin.[11]
Ikubese ya fara bayar da umarni a shekara ta 2019, a cikin wani shirin fim a TV series titled, Fim din mai suna: Kyaddala wanda kalmar Uganda ce da ke nufin "Ainihinta" lokacin da aka fassara kalmar.[12]
Ikubese ya lashe lambar yabo ta City People Movie Award for Most Promising actor of the Year a bikin bayar da kyauta na City People Entertainment Awards.[6]
Ikubese ya lashe lambar yabo ta zaman lafiya na shekara a bikin bayar da lambar yabo ta Peace Achievers.[4]
A shekarar 2019, Ikubese ya aure da ’yar kwalliyar Najeriya Anita Adetoye.[13][14][1]
Ikubese a wata hira da manema labarai na The Punch ya lissafa buga wasan ƙwallon kwando, wasan ƙwallon kafa da kuma dafa abinci a matsayin abin sha'awa.[15]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.