abin da kan iya halaka mutum idan aka ci ko aka sha From Wikipedia, the free encyclopedia
Dafi ko kuma Guba ana kiran dafi da turanci poison/venom dai kamar yadda masu ilimin biology suka bayyana yana nufin duk wani abinda yakeda haɗari wanda har zai iya sabbaba mutuwa ko jin rauni ko raunata wasu sassan jikin Ɗan Adam, misali gaɓoɓi koda kuwa dabbace ko kuma ɓata baki ɗayan jiki. Dafi yana samuwa ne kodai ta hanyar sara/cizon wani dabba misali maciji, ko kuma harbin kunama da ƙarinta (by sting or bite) sai dai shi dafin dabbar da take cizo yasha banban da sauran waɗansu dafin kasancewa shi ta sanadiyyar cizo ne ko harbi kalan wannan dafin na dabbobi ana kiranshi da Turanci da (Venoms)
dafi | |
---|---|
class of chemical substances by use (en) da cause of death (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Abubuwan sunadarai, noxa (en) , Makami da Q124326543 |
Amfani | poisoning (en) da Makami |
Has characteristic (en) | toxicity (en) da mode of toxic action (en) |
Tarihin maudu'i | history of poison (en) |
Amfani wajen | poisoner (en) |
Ga jerin su da harshen turanci kamar haka kowane tare da bayaninshi:
Dafi ko kuma guba yanada matuƙar haɗari ga duk wani mai rai kamar yadda ya gabata akan cewa kodai yayi sanadiyar mutuwar mai rai ko kuma ya lalata masa wasu gaɓoɓi. Misali binciken da akayi a shekara ta 2013 ya nuna dafi/guba ta kashe kusan mutum 57,000 Sai kuma a shekarar 1990 ya kashe kusan mutum 170,000 wanda kusan duk sanadin cizon maciji kunama da sauran dabbobi masu dafi, idan aka kwatanta da shekara ta 2013 ya ragu akan alƙalumman da aka samu a shekara ta 1990.[1] Duk da cewa a wani ɓangaren ana iya amfani da dafi don yin wani amfani na daban Ana amfani da guba ta hanyar magance ƙwari, haka wasu mutanen marasa imani ko kuma maƙetata suna amfani da guba don halaka abokan hamayyar su wanda wannan ya saɓawa Addinin Musulunci da kuma al'adun Hausawa don a musulunci duk wanda ya kuma kashe wani shima a kashe shi don kisan kai abu ne mai matuƙar haɗari duniya da lahira. Akanyi amfani da guba ta hanyar zubawa ƙwari a abincin su da dai sauran hanyoyin na daban.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.