Chioma Ubogagu
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Chioma Grace Ubogagu (an haife ta ne a 10 ga watan Satumban, a shekara ta alif 1992A.C)[1][2] ta kasan ce kuma ƙwararriyar 'yar wasan ƙwallon ƙafa ce wadda take taka leda a matsayin 'yar wasan gaba na Real Madrid CF a cikin Spanish Primera División.[3][4] Ta taba taka leda a Orlando Pride, Brisbane Roar, Houston Dash da Arsenal.[5][6][7] Ubogagu ta buga wasan kwallon kafa na jami'ar Stanford kuma ta buga wasanni a lokacin da take matashiya a matakai daban-daban a Amurka, inda ta lashe Kofin Duniya na mata na U-20 a shekarar 2012.[8][9][10]

Remove ads
Tarihin Rayuwa da Aiki
Ubogagu an haife ta ne a Landan, inda iyayenta suke da zama,[11][12][13] mahaifiyar ta Tina ma'aikaciyar jinya ce shi kuma mahaifinta Aloy ma'aikacin zamantakewar al'umma,[14][15][16] dukkanin su 'yan Najeriya ne da suka ƙaura Landan don neman damar aiki.[17][18][19] Tun tana shekara 3, iyayenta suka rabu inda hakan yass ta ƙaura tare da mahaifiyarta da babban yayanta zuwa Coppell,[20][21][22] Texas a wani yanki a cikin Dallas – Fort Worth metroplex inda a nan ne ta fara harkar kwallon kafa bayan ta shiga kungiyar ƙwallon ƙafa ta D'Feeters.[23][24][25]
Remove ads
Kungiyoyin da tayi Wasa

'Arsenal Ladies, 2015
Houston Dash, 2016
Orlando Pride, 2017–2019
Loan at Brisbane Roar
CD Tacón / Real Madrid, 2019 – yanzu
Wasanta a Mataki na Duniya
Saboda iyayenta da wurin haihuwarta, Ubogagu ta na da damar wakiltar Najeriya, Ingila ko Amurka. Ta zaɓi wakiltar Amurka a mataki na yarinta,[26][27][28] inda ta bugawa ƙasar wasanni a mataki na 'yan ƙasa da shekaru 18, 20 kuma 23.[29][30] A mataki na manyan 'yan wasa kuwa sai ta zaɓi wakiltar Ingila, ta hanyar karɓar tayin da aka mata a Oktoban 2018 kuma ta fara zama babbar fitacciya ƙasar Ingila ɗin ne a ranar 8 Nuwamban 2018.[31][32][33]
'Yan Uwa da Dangi


Kakanta Austin Eneuke ya buga wa Najeriya da Tottenham Hotspur wasa.[34][35] Ubogagu ta kasance masoyiyar Arsenal a duk sanda suke kallon wasan Arewacin London, duk da mahaifinta ya so rinjayarta da ta goyi bayan Tottenham.[36][37]
Ƙididdigar Wasanni
Kulab
Nasorinta a duniya
Remove ads
Lambobin Yabo
Ingila
- SheBelieves Cup : 2019
Bayanan kula
Manazarta
Hanyoyin haɗin waje
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads