Tijani Babangida
Dan Wasan kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Tijjani BabangidaTijani Babangida (Taimako·bayani) (an haife shi a ranar ashririn da biyar (25) ga watan Satumba (9), shekara ta alib dubu daya da dari tara da saba'in da uku "1973") shi ne tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriyawanda ya yi wasa a matsayin ɗan wasan gefe. An san shi da saurin sa, wani lokacin wasan sa ana kwatanta shi da na Marc Overmars. Babangida ya shafe mafi yawan shekarun wasan sa a Ajax. Gabaɗaya, ya taka leda a ƙasashe biyar a nahiyoyi uku. A matakin kulab, Babangida ya kwashe shekaru tara a kasar Netherlands, yana wasa a VVV-Venlo, Roda JC Ajax, da Vitesse. [1] Ya lashe Eredivisie tare da KNVB Cup sau biyu tare da na karshen.
Tijani Babangida | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Kaduna, 25 Satumba 1973 (50 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Abokiyar zama | Rabah | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ahali | Haruna Babangida da Dan Wasan kwallon kafa Ibrahim Babangida | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | wing half (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 69 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 169 cm |
Ya bugawa kasarshi wasanni sama da guda 30, ciki harda wasanni hudu a gasar cin kofin duniya ta shekara ta alif 1998, a kasar Faransa. Ya halarci wasanni biyu na Gasar cin Kofin Kasashen Afrika kuma ya ci Kofin Olympics tare da Najeriya a shekara ta alif 1996. Babangida ya fara buga wa kasa wasa ne a shekara ta alif 1994. Ya rasa matsayinsa a kungiyar tun kafin gasar cin kofin duniya na shekara ta 2002. Bayan ya kwashe shekaru biyu yana taka leda a wasan kwallon kafa na kasa da kasa, an sake kiran Babangida a cikin tawagar Najeriya don shirye-shiryen Gasar cin Kofin Afrika a shekara ta 2004 a Tunisia.