From Wikipedia, the free encyclopedia
Shaffaq Mohammed MBE (an haife shi 21 ga watan Yulin shekarar 1972)[1] ɗan siyasan Biritaniya ne wanda ya yi aiki a matsayin me ba na Liberal Democrats na Majalisar Turai (MEP) a mazaɓar Yorkshire da Humber daga shekara ta 2019 zuwa shekarar 2020.[2]
Shaffaq Mohammed | |||
---|---|---|---|
2 ga Yuli, 2019 - 31 ga Janairu, 2020 ← Mike Hookem District: Yorkshire and the Humber (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Mirpur (en) , 21 ga Yuli, 1972 (52 shekaru) | ||
ƙasa | Birtaniya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Sheffield (en) : business studies (en) The Sheffield College (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da community organization (en) | ||
Kyaututtuka | |||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Liberal Democrats (en) |
[3]An haifi Shaffaq Mohammed a yankin Kashmir da ke karkashin mulkin Pakistan. A watan Afrilun shekarar 1977 ya koma Sheffield kuma ya yi karatu a makarantar Park House kuma daga baya Ya kammala karatu sa a Jami'ar Sheffield.
Tsakanin shekara ta 2004 zuwa shekarar 2014 Mohammed ya yi aiki a matsayin kansila na Liberal Democrat a mazaɓar Broomhill Ward. Ya fito takara da Crookes Ward a shekara ta 2014 kuma Bai yi nasara ba. Ya dawo a matsayin kansila na Ecclesall Ward a shekara ta 2016 kuma an sake zabe shi a shekarar 2018.
An zabi Mohammed a matsayin shugaban kungiyar Liberal Democrat Group a majalisar birnin Sheffield a watan Mayun 2011.[4] Ya rasa wannan mukamin ne a lokacin da ya rasa kujerarsa na kansila a shekarar 2014. Bayan komawarsa majalisa an sake zabe shi a matsayin shugaban kungiya a watan Mayun 2016.[5]
A wurin taron Dissolution Honors na shekarar 2015 ne, aka nada Mohammed Memba na Order of the British Empire (MBE) "don hidimar siyasa" a matsayin kansila a Sheffield City Council. [6]
[7]Mohammed ya tsaya takarar karkashin jam'iyyar Liberal Democrat a zaben Sheffield Brightside da Hillsborough na shekarar 2016, inda ya zo na uku da kashi 6.1% na kuri'un da aka kada.
Ya kasance dan takarar jam'iyyar Liberal Democrat a mazabar Sheffield ta tsakiya a babban zaben shekarar 2017, ya zo na hudu.[8]
Mohammed ya yi aiki a matsayin memba na Liberal Democrats a Majalisar Turai (MEP) na yankin mazaɓar Yorkshire da Humber daga 2019 zuwa 2020.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.