Salafiyya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Salafiyya, ko salafiyya, sannan ana kiran ta da Akidar Salafiyya, wata nau'in da'awa ce dake kira zuwa ga bin tafarkin karni ukun farko na addinin musulunci[1][2][3][4] Salafiyya Archived 2023-09-30 at the Wayback Machine jagoranci na da'awa a tsakanin mabiya Sunnah a adddinin Musulunci[5] wanda ta samu asali daga kasar Misra a karshen karni na goma sha tara (19th century) a amatsayin martani ga yaduwar mulkin Turawa da siyasar su,[6][7][8][9][10] Wanda tushen da'awar yasamu ne daga Da'awar Wahhabiyawa na karni na goma sha takwas (18th) wanda keda asali a garin Najd wani yanki dake kasar Saudiya ayanzu.[11] Akidar na da'awar a sake dawowa ne zuwa al'adar salaf, wato karnoni ukun farko na Musulmai, wanda yahada da zamanin Annabi(Muhammad)S.A.W dana Sahabbansa, sai wadanda suka biyo bayan su (wato Tabi'ai), sannan kuma suma wadanda suka biyo bayan su (wato Taba Tabi‘in).[12]