Salaf
From Wikipedia, the free encyclopedia
Salaf (larabci|سلف, "magabata" ko "wadanda suka kasance kafin mu"), kuma kalmar ake nufi da "al-salaf al-ṣāliḥ" (larabci|السلف الصالح, "magabata shiryayyu") kuma sune wadanda suka kasance a karnoni uku na farkon Musulunci, wanda Manzon Allah yayi nuni dasu[Ana bukatan hujja], kuma sune kadai Mutanen da duniyar Musulmai ta yarda dasu amatsayin magabata na kwarai, duk wani malami da yazo bayansu to ba'a kiransa da wannan ma'anar na As-Salaf-alSalihin,[1] wadannan karnoni uku sune, karnin [Manzon Allah|Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agareshi]] da Sahabbansa, da wadanda sukazo bayansu (wato Tabi'ai), da suma wadanda suka biyosu (wato Tabi'ut Tabi‘in).[2]
![]() | |
---|---|
group of humans (en) ![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Musulmi |
Hannun riga da |
Q113996839 ![]() |
Dukkanin kalmomin Salaf, Saleef da Salafah duk suna danganta al'ummar Mutanen da suka gabace mu ne.[3].