Ramadan
From Wikipedia, the free encyclopedia
Ramadan (Larabci رمضان) Watan Musulunci ne na tara, kuma a cikin sa ne aka saukar da Alqur'ani ga Annabi Muhammad (s.a.w).
Ramadan | |
---|---|
calendar month (en) da Malayalam | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Hijri month (en) |
Mabiyi | Sha'ban |
Ta biyo baya | Shawwal |
Azumin Musulunci a watan Ramadan na daya daga cikin shika shikan Musulunci guda biyar. Musulmi kan azumci watan iyakar tsayin sa kullum tun daga fitowar alfijir har ya zuwa faduwar rana. Musulmi sunyi imani da fadin an saukar da Alkur'ani ne a watan na ramadan wanda ake yin wahayin sa a hankali a hankali daga Allah zuwa ga Annabi Muhammad (s.a.w) ta hannun dan aiken Allah Mala'ika Jibrilu. Annabi ya fada ma musulmai "Ana bude dukkannin kofofin Aljannah kuma ana kulle kofofin Jahannama tare da daure shaidanu a watan na Ramadan". Daga karshen watan ana gabatar da bikin karamar sallah.kuma wata ne da ake gabatar da sallah asham, raka goma. Ana yawaita sadaka da ayyukan alheri musamman musulmai masu neman rabauta da Duniya da lahira.[1]