Nabil Lasmari
From Wikipedia, the free encyclopedia
Nabil Lasmari (an haife shi a ranar 8 ga watan Fabrairu 1978) tsohon ɗan wasan badminton ne na Faransa- Algeriya.[1] A Faransa, ya buga wa Roubaix wasa, ya lashe gasar zakarun kasa na maza guda hudu a shekarun 1998, 2000, 2002 da 2004.[2][3] Yayin da yake wakiltar Aljeriya, Lasmari ya lashe gasar cin kofin Afrika a shekarun 2006 da 2007, da kuma 2007 All-Africa Games.[4] [5] Ya halarci gasar Olympics ta shekarar 2008 a birnin Beijing na kasar Sin. [6] Yanzu yana aiki a matsayin koci a kulob din Chantecler a Bordeaux, Faransa. [7]
Quick Facts Rayuwa, Haihuwa ...
Kulle