From Wikipedia, the free encyclopedia
Maulidi asali dai kalmar larabci ce mai asali da kalmar “Milad”, aka arota daga Larabci zuwa Hausa, kalmar na nufin Haihuwa ko kuma Murnar Haihuwa, Maulidi wani biki ne da Musulmai mabiya ɗarikun Sufaye da kuma ƴan Shi’a ke yi duk shekara don tunawa da haihuwar Manzo Allah, Annabi Muhammad(SAW). Ana yin Maulidi ne a duk ranar 12 ga watan Rabi' al-awwal ta shekarar Hijira. Musulmi a fadin duniya ne ke bikin maulidin kuma suna fitowa domin bayyana farin cikinsu.[1][2]
| |
Suna a harshen gida | (ar) اَلْمَوْلِدُ النَّبَوِيُّ |
---|---|
Iri |
Islamic holidays (en) Sufi terminology (en) religious and cultural festive day (en) |
Rana | 12 Rabi' al-awwal (en) |
Bisa | prophetic biography (en) |
Al'ada | Islamic culture (en) da Arab culture (en) |
Wuri |
Duniyar Musulunci Arab world (en) |
Harshen aiki ko suna | Larabci da multilingualism (en) |
Addini | Musulunci da Sufiyya |
Cultural heritage (en) | |
Matsalar Lua: expandTemplate: template "Protecció patrimonial/prepara" does not exist. |
Wasu kasashen musulmi da suke bayar da kuma hutu don bikin murnar Maulidi sun hada da:anahin shine bayan shekar zagayo (saw) Muhammad
Amman wasu daga cikin Musulmai sun ce basu yarda da Maulidi ba, kasancewar yadda suke ganin cewar bikin kirkirarre ne, kuma baida asali daga Manzon Allah (SAW), kasan cewar bai aikata ba, kuma a ganinsu ba shi da asali acikin addinin Musulunci. Daga cikin malamai masu irin wannan fahimta akwai:
Wasu daga mabiya Ahlus-Sunnah wal-Jama'ah bangaren Salafiyya basa bin tsarin yin Maulidi. Daga ciki harda kasar Saudi Arebiya, inda aka Haifi Manzon Allah, a kasar Najeriya akwai kungiya mai zaman kanta mai suna Izalatul bidi'a wa'ikamatus sunna, kungiyace dake wa'azi akan kawar da bidi'o'i da kuma tsaida sunna wacce Abubakar Mahmud Gumi ya kirkira. Suna da reshe a Kaduna. Duk daya ke Annabi bai aikata ba amma, idan ya hana shi ne hujja kamar yadda ayyoyin Al-Qur'ani suka nuna. Kuma idan muka lura dacewar dole sai komai Annabi ya aikata zamuyi. Toh muna bukatar amsoshi da dama kamar; 1. Annabi yayi amfani da wayar hannu 2. Yaje makkah a jirgi 3. Ya kira Sallah da sifika 4. Ya sa fanka ko a.c a masallaci 5. Ya hau mota. Da dai sauran su, kuma idan mukai duba da wasu abubuwa addinin Musulunci bazai cigaba ba sai da su kamar zuwa aikin hajji a jirgi, kamar shiga mota saboda ya da Musulunci da dai sauran su. Allah shine masani.
Sai dai mabiya darikun sufaye da suka hada da Qadiriyya, Tijjaniyya da kuma mabiya Shi’a da suke danganta kansu ga Imamu Ali suna bikin Maulidin. Ana karatun Al’kur’ani da kuma jawabai na tarihi da fadakarwa ne a guraren taron; hade da shagulgulan walima da wakokin yabo ga Manzon Allah (s.a.w) don bayyana farin ciki.
Wasu malaman da suke ganin dacewar bikin Maulidin sun hada da:
.[6][7][8][9][10][11][12][13][10][14][15][16][10][17][18][19][20][21]
Akwai kuma malamai da suke ganin bikin Maulidi ya danganta da niyyar mai yi ne. Idan aka saka abubuwan da shari’a ta hana to bikin ya haramta. Amma idan aka yi shi don farin ciki da Manzon Allah (saw) to wannan za a samu ladan niyya. Daga cikin masu wannan mahanga akwai:
• Sheikh Ahmad Ibn Taimiyya [22]
• Sheikh Usman Danfodiyo
• Sheikh Abdallah bn Bayyah [23]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.