![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/82/Mali_map.png/640px-Mali_map.png&w=640&q=50)
Matsalolin muhalli a Mali
From Wikipedia, the free encyclopedia
Abubuwan da suka shafi muhalli a Mali, sun haɗa da kwararruwar hamada, Sare Dazuka, zaizayar ƙasa, fari, da rashin wadataccen ruwan sha. Sare dazuzzuka matsala ce ta musamman kuma mai girma. A cewar ma'aikatar muhalli, al'ummar ƙasar Mali na cin ton miliyan 6 na itace a duk shekara domin yin katako da kuma man fetur. Domin biyan wannan buƙata, ana yin asarar murabba'in kilomita 4,000 a duk shekara, wanda kusan ke tabbatar da lalacewar gandun daji na ƙasar.
![]() | |
---|---|
aspect in a geographic region (en) ![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Abubuwan da suka shafi muhalli |
Facet of (en) ![]() | Abubuwan da suka shafi muhalli |
Ƙasa | Mali |
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/82/Mali_map.png/320px-Mali_map.png)
Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka shafi muhalli a Mali shi ne kwararowar hamada. Ƙasar Mali ta faɗa cikin fari shekaru da dama a yanzu kuma hakan yana shafar ƙasar. Zaizayar ƙasa, sare dazuzzuka, da asarar wuraren kiwo, duk manyan matsaloli ne a Mali. Mali kuma tana da ƙarancin ruwa.[1]
Don taimakawa wajen ɗorewar matsalar da ke ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar Mali gwamnati ta ware kashi 3.7 cikin 100 na ɗaukacin yankin ƙasar ta Mali. Ta amince da yarjejeniyoyin muhalli na ƙasa da ƙasa da suka shafi bambancin halittu, sauyin yanayi, kwararowar hamada, nau'ukan da ke cikin haɗari, da kuma kariya ta fuskar ozone . [2]
A cewar hukumar ta FAO, kashi 10.2% ko kuma kusan hekta 12,490,000 na ƙasar Mali na da dazuzzuka. Mali tana da dajin da aka shuka hekta 530,000. Canjin dazuzzukan : Tsakanin shekarar 1990 da ta 2010, Mali ta yi asarar matsakaicin ha 79,100 ko kuma 0.56% a kowace shekara, jimilla ta yi hasarar 11.2%, ko kuma kusan 1,582,000 ha, a wannan lokacin. Ƙasar Mali tana da maki 7.16/10 a shekarar 2018, inda take matsayi na 51 a duniya cikin kasashe 172.[3]