![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/7/7b/Tostan_English_Wordmark_clear_RBG.png/640px-Tostan_English_Wordmark_clear_RBG.png&w=640&q=50)
Kungiyar Tostan
From Wikipedia, the free encyclopedia
Tostan (ma'ana "nasara" a cikin Wolof ) rajista ce ta Amurka mai lamba 501 (c) (3) ta kasa da kasa mai hedikwata a Dakar, Senegal . Manufar kungiyar ita ce "karfafawa al'ummomi cigaba da cimma burinsu na nan gaba da kuma karfafa gungun manyan kungiyoyi da ke haifar da martaba ga kowa" a kasashen Afirka ta Yamma da dama, da suka hada da Senegal, Guinea, Guinea-Bissau, Gambiya, Mali, da Mauritaniya .
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Iri |
nonprofit organization (en) ![]() |
Ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mulki | |
Hedkwata | Dakar |
Tsari a hukumance |
501(c)(3) organization (en) ![]() |
Financial data | |
Haraji | 8,152,895 $ (2016) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1991 |
tostan.org |
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Iri | NGO |
Ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mulki | |
Hedkwata | Dakar |
Tsari a hukumance |
501(c)(3) organization (en) ![]() |
Financial data | |
Haraji | 8,152,895 $ (2016) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1991 |
tostan.org |
Tostan ta dauki cikakkiyar hanya, hadaddiyar hanya ta ci gaba ta hanyar sauƙaƙa shirye-shiryen haƙƙin ɗan adam, shirye-shiryen ilimi ba na yau da kullun ba, galibi Shirin al'umma (C.E.P), wanda ke nufin tallafawa da ƙarfafa mahalarta da al'ummomi don jagorancin ci gaban su. kungiyarr tana ɗaukar sama da mutane 500 aiki kuma tana aiki don haɓakawa da haɓaka haɗin kan al'umma a cikin ayyukan da suka shafi karatu da rubutu, kiwon lafiya da tsafta, jin daɗin yara, haƙƙin ɗan adam da dimokiradiyya, ɗorewar muhalli, da ƙarfafa tattalin arziƙi.
Koda yake kuma an san Tostan da nasarar da ta samu wajen hanzarta yin watsi da al'adun gargajiya masu cutarwa, musamman yankan mata da auren yara, a duk faɗin Afirka, kungiyar ta kuma sami nasarori masu kyau a fannonin tasirin mulki, ilimi, kiwon lafiya, ƙarfafa tattalin arziƙi, da mahalli, cigab kasar, haka kuma a cikin lamuran da suka shafi kare yara, karfafawa mata da ‘yan mata, da bunkasa kananan yara. A shekara ta 2007, Tostan ta sami lambar yabo ta Conrad N. Hilton ta Jin kai, kyauta mafi girma a duniya, saboda "gagarumar gudummawar da ta bayar wajen rage radadin wahalar dan adam." [1]