From Wikipedia, the free encyclopedia
Katsina, mai yiwuwa kalmar daga "Tamashek" (yana nufin ɗa ko jini) ko mazza (maza) tare da "inna" (uwa). Karamar hukuma ce kuma babban birnin Jihar Katsina, Arewacin Najeriya. Katsina tana da nisan kilomita 260 km (160 mil) daga gabashin Birnin Sokoto, da kuma kilomita 135 Km (84 mil) daga Arewa Maso Yammacin Birnin Kano, tana kusa da iyakar ƙasar Nijar.
An ƙiyasta yawan mutanen Birnin Katsina a shekare ta 2016 da kimanin mutum 429,000.[1]
Birnin ya kasance cibiyar noma da kiwo inda ake noman gyaɗa da auduga da fatu da gero da kuma dawa,[2] sannan har ila yau, akwai masana'antun sarrafa man-gyaɗa, da ƙarafa, sannan birnin ya kasance cibiyar kiwon dabbobi kamar su shanu, tumakai, awakai da kaji.
Mafi akasarin mutanen birnin Musulmai ne daga ƙabilar Hausa da Fulani.
Tsohon shugaban kasan Najeriya Umaru Musa Yar'Adua ya kasance babban mutum ne daga Katsina.[3]
Gwamna mai ci na yanzu a Jihar Katsina shi ne Aminu Bello Masari,[4] wanda aka rantsar a matsayin gwamnan jihar a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015, wanda ya gaji kujerar daga hannun Bar. Ibrahim Shema.[5]
Fadar Sarkin Katsina wanda akafi sani da "Gidan Korau" wani katafaren gini ne da ke tsakiyar tsohon birnin. Fadar ta kasance muhimmin alama na daga al'adu, tarihi da kuma dabi'un Katsinawa. Kamar yadda tarihi ya nuna, Muhammadu Korau ya gina fadar a shekara ta 1348 CE, wanda ake tsammani cewa shi ne sarki musulmi na farko a Katsina. Wannan ne yasa ake kiran masarautar da Gidan Korau. Fadar na ɗaya daga cikin gidan sarauta mafi tsufa kuma na farko-farko, tare da masarautun Daura, Kano Zazzau. Masarutar zagaye take da ganuwa wato katangar gidan sarki wanda a yanzu babu ita. Kofar da ke isa zuwa masarautar ita ce 'Kofar Soro' sannan kuma kofar da ke bayan ta ita ce 'Kofar Bai' (babu ita a yanzu). Fadar sarkin a cikin masarutar wani ƙayataccen gini ne mai ƙirar salo na gargajiya.[6] Sarkin Katsina na yanzu shi ne Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, daga dangin sarakunan Fulani.
Birnin na zagaye da ganuwa mai tsawon kilomita 21 (mil 13) wanda ake tsammani an gina ta a ƙarni na 1100.[7] Kafin zuwan addinin musulunci, jagorar Katsina na musamman shi ne Sarki, wanda yake fuskantar kisa a duk lokacin da aka same shi baya mulki yadda ya kamata. Daga ƙarni na 17 zuwa ƙarni na 18, Katsina ta kasance cibiyar kasuwanci na Ƙasar Hausa kuma ta zamo mafi girma daga cikin ƙasashen Hausa Bakwai. Fulani sun mamaye Katsina a lokacin Jihadin Fulani a shekarar 1807. A shekarar 1903 ne, sarkin Katsina na lokacin Abubakar ɗan Ibrahim ya miƙa wuya ga mulkin Turawa, wadda ta ci gaba har zuwa samun 'yanci kai a shekarar 1960.
A lokacin kasuwancin yankunan kusa da Sahara na Afurka, birnin ya kasance mai albarka kuma muhimmin cibiyar kasuwanci, kuma ana daukanta a matsayin mafi shahara ta fuskar cinikayya, kasuwanci da kuma baiwar sarrafe-sarrafe. Matafiyi ɗan kasar Jamus, Friedrich Hornemann ne bature na farko da ya fara isa birnin a ƙarni na 19.
Tarihin birnin dangane da ilimin boko ya samo asali ne tun daga farkon shekarun 1950, a yayin da aka gina makaranta ta matsakaita ta farko a arewacin Najeriya. Akwai manyan makarantu a yanzu wanda suka haɗa da jami'oi guda biyu, Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da kuma ta 'yan kasuwa wato Jami'ar Al-Qalam Katsina; sannan kuma akwai politakanik wato Hassan Usman Katsina Polytechnic da kuma Federal College of Education, Katsina.Har wayau, birnin gida ne ga shahararren masallacin karni na 18 wato Hasumiyar Gobarau, hasumiya mai tsawon mita 15 (50 ft) wanda aka gina da laka da itacen dabino.
A cikin watan Disambar shekarar 2020, aka yi garkuwa da yara 300 'yan makaranta a Kankara.[8] Amma daga bisani an maido da yara 344 mako ɗaya bayan hakan.[8] Ƙungiyar Boko Haram ta yi iƙirarin cewa ita ta aikata hakan, amma jami'ai sun nuna rashin amincewa da hakan kasancewa babu ƙungiyar Boko Haram a yankin.[9]
Dangane da rabe-raben yanayi na Koppen, Katsina ta faɗa acikin yanayi na zafi wato semi-arid climate, wanda ake rubuta wa a takaice da BSh a taswirorin yanayi na duniya.[10]
Akwai ƙarancin ruwan sama a birnin Katsina, babu rikodin na ruwa kwata kwata a tsakanin watannin Nuwamba zuwa March.
S/N | Code | Shekaru | Junairu | Febreru | March | Aprelu | Mayu | Yuni | Yuli | Agusta | Satumba | Oktoba | Nuwamba | Disemba |
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
1. | 65028 | 1990 | 0 | 0 | 0 | 0 | 29.9 | 57.9 | 198.8 | 220.2 | 34.7 | 0 | 0 | 0 |
2. | 65028 | 1991 | 0 | 0 | 10.8 | 12.2 | 73.5 | 58.8 | 71.5 | 109.7 | 21.1 | 1.4 | 0 | 0 |
3. | 65028 | 1992 | 0 | 0 | 0 | 0 | 33.6 | 19.9 | 89.3 | 119.4 | 70.7 | 0.2 | 0 | 0 |
4. | 65028 | 1993 | 0 | 0 | 0 | 0 | 4.5 | 42.3 | 69 | 94.5 | 51.7 | 0 | 0 | 0 |
5. | 65028 | 1994 | 0 | 0 | 0 | 3.1 | 12.3 | 42.3 | 107.9 | 174.2 | 113.1 | 20.3 | 0 | 0 |
6. | 65028 | 1995 | 0 | 0 | 0 | 10 | 30 | 70 | 80 | 120 | 80 | 10 | 0 | 0 |
7. | 65028 | 1996 | 0 | 0 | 0 | 0 | 42.6 | 44.5 | 38.1 | 66.8 | 67.8 | 0 | 0 | 0 |
8. | 65028 | 1997 | 0 | 0 | 7.2 | 9.5 | 89.5 | 30.4 | 91.1 | 153.7 | 56.5 | 8.3 | 0 | 0 |
9. | 65028 | 1998 | 0 | 0 | 0 | 10.1 | 11.4 | 43.4 | 114.1 | 116.6 | 135.2 | 0.8 | 0 | 0 |
10. | 65028 | 1999 | 0 | 0 | 0 | 0 | 4.2 | 22.4 | 149.2 | 89.8 | 132.3 | 18.4 | 0 | 0 |
11. | 65028 | 2000 | 0 | 0 | 0 | 0 | 1.6 | 106.8 | 299.9 | 160.2 | 62.1 | 45 | 0 | 0 |
12. | 65028 | 2001 | 0 | 0 | 0 | 16.9 | 83.9 | 110.8 | 176 | 240.9 | 70.6 | 0 | 0 | 0 |
13. | 65028 | 2002 | 0 | 0 | 0 | 0 | 2.9 | 141.3 | 170.4 | 71.3 | 199.1 | 9.8 | 0 | 0 |
14. | 65028 | 2003 | 0 | 0 | 0 | 4 | 52.8 | 57.2 | 118.2 | 275.5 | 75.1 | 16.4 | 0 | 0 |
15. | 65028 | 2004 | 0 | 0 | 0 | 0 | 74.9 | 151.2 | 161.1 | 268.8 | 42 | 0 | 0 | 0 |
16. | 65028 | 2005 | 0 | 0 | 0 | 14.8 | 18.4 | 83.2 | 173.7 | 216.1 | 194 | 50.4 | 0 | 0 |
17. | 65028 | 2006 | 0 | 0 | 0 | 0 | 26.1 | 69.9 | 170.9 | 314.9 | 129.7 | 15 | 0 | 0 |
18. | 65028 | 2007 | 0 | 0 | 0 | 6.2 | 84.9 | 135.2 | 117.4 | 314.9 | 45.5 | 0 | 0 | 0 |
19. | 65028 | 2008 | 0 | 0 | 0 | 16.6 | 8.5 | 63.3 | 182.9 | 213.9 | 67.7 | 4.2 | 0 | 0 |
20. | 65028 | 2009 | 0 | 0 | 0 | 0 | 95 | 57.9 | 96.5 | 123.3 | 38.3 | 29 | 0 | 0 |
21. | 65028 | 2010 | 0 | 0 | 0 | 85.6 | 8.1 | 118.8 | 226.1 | 448.9 | 76.6 | 48.6 | 0 | 0 |
22. | 65028 | 2011 | 0 | 0 | 0 | 0 | 38 | 149.2 | 116.6 | 180.6 | 67.3 | 8 | 0 | 0 |
23. | 65028 | 2012 | 0 | 0 | 0 | 0 | 59.5 | 135.2 | 117.4 | 314.9 | 129.7 | 15 | 0 | 0 |
24. | 65028 | 2013 | 0 | 0 | 0 | 42.4 | 36.7 | 103.2 | 89 | 274.7 | 107.6 | 10.2 | 0 | 0 |
25. | 65028 | 2014 | 0 | 0 | 0 | 0 | 38.1 | 39.5 | 178.9 | 178.7 | 46.3 | 0 | 0 | 0 |
26. | 65028 | 2015 | 0 | 0 | 0 | 0 | 0 | 89.1 | 178.9 | 274.7 | 46.3 | 9 | 0 | 0 |
27. | 65028 | 2016 | 0 | 0 | 0 | 0 | 4.5 | 42.3 | 69 | 94.5 | 59.5 | 0 | 0 | 0 |
28. | 65028 | 2017 | 0 | 0 | 0 | 10.1 | 11.4 | 62 | 114.1 | 16.6 | 135.2 | 0.8 | 0 | 0 |
29. | 65028 | 2018 | 0 | 0 | 0 | 0 | 2.9 | 141.3 | 170.4 | 149.7 | 199.1 | 63.8 | 0 | 0 |
30. | 65028 | 2019 | 0 | 0 | 0 | 11.6 | 8.1 | 118.8 | 232.7 | 359.1 | 98.6 | 26.6 | 0 | 0 |
Tushe: Hukumar Kula da Yanayi, Katsina (NiMET) 2021.
Yanayi na nufin yanayi na zafi ko kuwa yanayin sanyi na wuri
Katsina na da yanayi na zafi sosai, tare da watan Aprelu a matsayin wata mafi zafi na kimanin 40.8 °C ko kuma 105.4 °F, tare da yanayi na matsakaicin zafi (31.4 °C or 88.5 °F) acikin watan December.[11]
S/N | Code | Shekara | Junairu | Febrelu | March | Aprelu | Mayu | Juni | Juli | Augusta | Satumba | Oktoba | Nuwamba | December |
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
1. | 65028 | 1985 | 31.7 | 29.7 | 36.5 | 36.5 | 38.6 | 35.9 | 31.6 | 31.3 | 33.2 | 35.5 | 33.9 | 28.2 |
2. | 65028 | 1986 | 38.9 | 34.7 | 37 | 40.2 | 39.2 | 37 | 31.5 | 31.4 | 32.2 | 35.4 | 33.3 | 37.4 |
3. | 65028 | 1987 | 30.4 | 33.6 | 36 | 37.6 | 40.1 | 36.6 | 35.1 | 32.6 | 34.4 | 35.7 | 34.1 | 30.1 |
4. | 65028 | 1988 | 28.4 | 32 | 36.7 | 39 | 39.2 | 35.3 | 31.9 | 29.5 | 31.9 | 34.3 | 33.7 | 28.5 |
5. | 65028 | 1989 | 26 | 28.4 | 35.2 | 39.3 | 38.3 | 36.2 | 32.4 | 30.9 | 32.6 | 33.6 | 33.6 | 29.6 |
6. | 65028 | 1990 | 32.2 | 30.1 | 33.5 | 39.9 | 38.1 | 36.7 | 31.7 | 31.4 | 33.9 | 36.7 | 35.5 | 34 |
7. | 65028 | 1991 | 29.4 | 35.9 | 35.9 | 39 | 35.3 | 35.1 | 31 | 30.5 | 34.4 | 36.4 | 33.3 | 28.9 |
8. | 65038 | 1992 | 29.1 | 30.1 | 36.4 | 39 | 36.5 | 35.6 | 31 | 30.3 | 32.4 | 35.7 | 31.5 | 30.2 |
9. | 65028 | 1993 | 36.5 | 32.5 | 36.5 | 39.3 | 39.3 | 36.5 | 33.3 | 31.5 | 33.1 | 36.9 | 35.5 | 29.5 |
10. | 65028 | 1994 | 29.5 | 31.6 | 38.2 | 38.7 | 38.9 | 35.4 | 31.8 | 29.5 | 31.4 | 34.1 | 32.3 | 27.4 |
11. | 65028 | 1995 | 27.7 | 31 | 38.1 | 38.8 | 38.3 | 36.1 | 32.9 | 30.9 | 32.6 | 35.4 | 32.2 | 31.7 |
12. | 65028 | 1996 | 32.1 | 34.8 | 37.6 | 39.3 | 38.3 | 34.5 | 33.6 | 30.3 | 32.3 | 35.3 | 31.2 | 31.8 |
13. | 65028 | 1997 | 31.3 | 28.5 | 34.8 | 38.3 | 36.5 | 35.1 | 32.4 | 31.7 | 33.6 | 36.5 | 35.6 | 30.4 |
14. | 65028 | 1998 | 29.4 | 33.5 | 33.9 | 40.2 | 39.3 | 35.6 | 32.1 | 30.8 | 31.6 | 34.9 | 34.9 | 30.6 |
15. | 65028 | 1999 | 30.8 | 34 | 39 | 39.5 | 39.3 | 38.1 | 31.7 | 29.5 | 31.4 | 33.4 | 33.2 | 29.7 |
16. | 65028 | 2000 | 31 | 28.6 | 35.2 | 40.5 | 39.6 | 35.3 | 31 | 31 | 32.9 | 33.8 | 33.8 | 29.6 |
17. | 65028 | 2001 | 29.3 | 30.4 | 36.9 | 38 | 37.8 | 34.3 | 31.3 | 30 | 32 | 34.8 | 33.6 | 31.9 |
18. | 65028 | 2002 | 26.3 | 31.6 | 37 | 39.8 | 40.8 | 36 | 32.5 | 31.1 | 32.2 | 32.4 | 33.8 | 31 |
19. | 65028 | 2003 | 34.7 | 35.3 | 39.6 | 39.4 | 34.4 | 35.6 | 31.3 | 30.8 | 32.8 | 33.8 | 33.5 | 31.7 |
20. | 65028 | 2004 | 32 | 29.9 | 40 | 39 | 36.5 | 32 | 30 | 33 | 36 | 34 | 33.9 | 31.9 |
21 | 65028 | 2005 | 13.4 | 19.4 | 22 | 24 | 25.2 | 24.2 | 22.7 | 21.6 | 22.3 | 20 | 16.2 | 14 |
22. | 65028 | 2006 | 15 | 18.1 | 20 | 21.4 | 26 | 25 | 23.2 | 22 | 22.2 | 22 | 15 | 11.8 |
23. | 65028 | 2007 | 12.8 | 13.6 | 18.3 | 22.7 | 24.4 | 23.8 | 21.5 | 20.3 | 20.5 | 17.6 | 13.3 | 10.7 |
24. | 65028 | 2008 | 9.5 | 14.4 | 20 | 21.2 | 23.2 | 22.8 | 21.1 | 19.5 | 19.8 | 17.5 | 13.3 | 11.5 |
25. | 65028 | 2009 | 11.1 | 14.2 | 19.2 | 23.4 | 24.2 | 22.4 | 22.4 | 21.1 | 22.1 | 21.5 | 14.6 | 13.6 |
26. | 65028 | 2010 | 14.5 | 17 | 19.7 | 23.8 | 23.7 | 23.8 | 22 | 20.7 | 21.9 | 19.6 | 14.3 | 14.1 |
27. | 65028 | 2011 | 13.3 | 17.9 | 17.5 | 22.3 | 24.7 | 23.8 | 20.6 | 20.5 | 21.2 | 21.2 | 16.1 | 12.2 |
28. | 65028 | 2012 | 12.6 | 16.4 | 18.6 | 25.4 | 26.3 | 23.4 | 21.3 | 20.4 | 21.8 | 22.1 | 19.0 | 14.6 |
29. | 65028 | 2013 | 30.7 | 34.3 | 39.8 | 37.8 | 38.8 | 35.6 | 32.5 | 29.9 | 32.8 | 34.9 | 34.9 | 31.1 |
30. | 65028 | 2014 | 30.8 | 32.2 | 37.5 | 39.7 | 37.6 | 36.6 | 33.4 | 30.7 | 32.5 | 35.9 | 34.8 | 30.7 |
31. | 65028 | 2015 | 28.2 | 35.1 | 36.1 | 37.5 | 40.3 | 37.4 | 33.4 | 33.1 | 32.5 | 35.9 | 33.3 | 36.1 |
32. | 65028 | 2016 | 28.2 | 32.5 | 38.5 | 40.5 | 39 | 35.1 | 32.2 | 30.9 | 32.3 | 36.5 | 35.5 | 30.7 |
33. | 65028 | 2017 | 27.8 | 31.6 | 37.5 | 39.5 | 39 | 34.7 | 31.9 | 31 | 32.9 | 35.7 | 34.1 | 30.2 |
Tushe: Hukumar Kula da Yanayi Reshen Jihar Katsina (NiMET), 2021.
Watan Janairu shi ne wata mafi sanyi a Katsina tare da kimanin 14.7 °C or 58.5 °F.
S/N | Code | Shekara | Junairu | Febrelu | March | Aprelu | Mayu | Juni | Juli | Augusta | Satumba | Oktoba | Nuwamba | December |
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
1. | 65028 | 1985 | 16 | 14.7 | 22.6 | 24.2 | 26.7 | 24.4 | 22.2 | 22.2 | 22.6 | 21 | 17.5 | 14.7 |
2. | 65028 | 1986 | 12.7 | 18 | 23.4 | 26.2 | 26.6 | 25.2 | 21.9 | 21.8 | 22.2 | 20.8 | 17.9 | 12.8 |
3. | 65028 | 1987 | 13.1 | 16.7 | 21.4 | 22.3 | 25.2 | 24.9 | 23.9 | 22.6 | 23.6 | 22.5 | 17.5 | 14.5 |
4. | 65028 | 1988 | 14.4 | 16.4 | 21.6 | 26.6 | 24.5 | 24.5 | 22.7 | 21.2 | 22.3 | 19.6 | 16.2 | 13.5 |
5. | 65028 | 1989 | 11.1 | 13.8 | 18.9 | 23.1 | 25.1 | 24.4 | 22.2 | 21.7 | 22.8 | 20.6 | 15.8 | 13.8 |
6. | 65028 | 1990 | 15.5 | 14.3 | 17 | 25.7 | 25.7 | 25.1 | 22.4 | 25.8 | 23.4 | 21 | 18.1 | 17.4 |
7. | 65028 | 1991 | 13.7 | 18.9 | 21.7 | 25.5 | 24.5 | 24.4 | 16.2 | 12.6 | ||||
8. | 65028 | 1992 | 12.5 | 13.9 | 21.9 | 24.4 | 25.1 | 23.7 | 21.4 | 21.1 | 21.6 | 20.3 | 16.5 | 12.7 |
9. | 65028 | 1993 | 11.3 | 15 | 19.7 | 22.7 | 24.9 | 23.1 | 21.1 | 20.7 | 21.1 | 20.5 | 17.5 | 12.5 |
10. | 65028 | 1994 | 12.5 | 13.5 | 19.5 | 23.7 | 24.2 | 22.1 | 20 | 19.1 | 19.6 | 20.7 | 13.5 | 10.5 |
11. | 65028 | 1995 | 11.2 | 13 | 19.1 | 22.7 | 23.5 | 22.2 | 20.5 | 19.4 | 19.7 | 19.8 | 14 | 12.4 |
12. | 65028 | 1996 | 11.4 | 14.2 | 18.7 | 20.8 | 22.3 | 20.6 | 20 | 18.8 | 19 | 18.7 | 11.8 | 12.2 |
13. | 65028 | 1997 | 14 | 14.1 | 21.1 | 24.7 | 24.6 | 24 | 22.9 | 22.3 | 23.1 | 23.5 | 18.9 | 14.2 |
14. | 65028 | 1998 | 13.7 | 17.5 | 18.6 | 25.8 | 27.7 | 24.5 | 23.1 | 21.8 | 22.3 | 21.3 | 16.9 | 13.3 |
15. | 65028 | 1999 | 12.6 | 16 | 20.2 | 23.1 | 24.7 | 24.1 | 20.8 | 20.4 | 20.7 | 19 | 15.1 | 11.3 |
16. | 65028 | 2000 | 13 | 11.2 | 16.7 | 19 | 24.3 | 23.5 | 21 | 21 | 21.9 | 19.9 | 14.1 | 11 |
17. | 65028 | 2001 | 20.2 | 12.6 | 16.5 | 23 | 24.6 | 23.2 | 22 | 21 | 21.9 | 19.7 | 14.6 | 12.8 |
18. | 65028 | 2002 | 11.7 | 13.5 | 20 | 25.6 | 26 | 24 | 22.1 | 21.9 | 22.3 | 19.8 | 13.9 | 12.8 |
19. | 65028 | 2003 | 16.5 | 18.6 | 24.4 | 24 | 23.6 | 23.5 | 22.2 | 22.1 | 22.5 | 19.9 | 14.5 | 12.5 |
20. | 65028 | 2004 | 16 | 17.5 | 25 | 25 | 24.2 | 22 | 21 | 22 | 20 | 17 | 14.7 | 12.3 |
21 | 65028 | 2005 | 13.4 | 19.4 | 22 | 24 | 25.2 | 24.2 | 22.7 | 21.6 | 22.3 | 20 | 16.2 | 14 |
22 | 65028 | 2006 | 15 | 18.1 | 20 | 21.4 | 26 | 25 | 23.2 | 22 | 22.2 | 22 | 15 | 11.8 |
23. | 65028 | 2007 | 12.8 | 13.6 | 18.3 | 22.7 | 24.4 | 23.8 | 21.5 | 20.3 | 20.5 | 17.6 | 13.3 | 10.7 |
24. | 65028 | 2008 | 9.5 | 14.4 | 20 | 21.2 | 23.2 | 22.8 | 21.1 | 19.5 | 19.8 | 17.5 | 13.3 | 11.5 |
25. | 65028 | 2009 | 11.1 | 14.2 | 19.2 | 23.4 | 24.2 | 22.4 | 22.4 | 21.1 | 21.1 | 21.5 | 14.6 | 13.6 |
26. | 65028 | 2010 | 14.5 | 17 | 19.7 | 23.8 | 23.7 | 23.8 | 22 | 20.7 | 21.9 | 19.6 | 14.3 | 14.1 |
27. | 65028 | 2011 | 13.3 | 17.9 | 17.5 | 22.3 | 24.7 | 23.8 | 20.6 | 20.5 | 21.2 | 21.2 | 16.1 | 12.2 |
28. | 65028 | 2012 | 12.6 | 16.4 | 18.6 | 25.4 | 26.3 | 23.4 | 21.3 | 20.4 | 21.8 | 22.1 | 19.0 | 14.6 |
29. | 65028 | 2013 | 14.3 | 15.8 | 22.1 | 23.4 | 24.3 | 22.7 | 21.9 | 21 | 22.3 | 20.9 | 18.3 | 15.9 |
30. | 65028 | 2014 | 14.3 | 16.7 | 21.7 | 25.8 | 25.8 | 26.7 | 24.2 | 22.1 | 22.3 | 20.7 | 18.2 | 14.2 |
31. | 65028 | 2015 | 12.3 | 18.1 | 20.8 | 22.2 | 26.6 | 24.8 | 22.7 | 22.3 | 23.3 | 17.6 | 13.3 | |
32. | 65028 | 2016 | 13.5 | 16.5 | 24.2 | 27.1 | 26.8 | 24.9 | 23.2 | 22.2 | 22 | 22.3 | 18.7 | 13.1 |
33. | 65028 | 2017 | 13.4 | 16.4 | 19.9 | 25 | 27.1 | 24.8 | 23.1 | 22.4 | 23.1 | 19.9 | 16.6 | 15.4 |
Tushe: Hukumar Kula da Yanayi Reshen Jihar Katsina, (NiMET) 2021
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.