![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/3/39/Faculty_of_Medicine%252C_Obafemi_Awolowo_University%252C_Ile-Ife%252C_Osun_State%252C_Nigeria_%252812998041954%2529.jpg/640px-Faculty_of_Medicine%252C_Obafemi_Awolowo_University%252C_Ile-Ife%252C_Osun_State%252C_Nigeria_%252812998041954%2529.jpg&w=640&q=50)
Ifẹ
From Wikipedia, the free encyclopedia
Ifẹ̀ (Yoruba, ko kuma Ilé-Ifẹ̀) tsohon birni ne na Yarbawa da ke kudu maso yammacin Najeriya. Birnin na karkashin jihar Osun ta yau. Ife na da nisan kilomita 218 daga arewa maso gabas da Legas [1] yana da yawan jama'a 509,813, mafi girma a jihar Osun bisa ga ƙidayar yawan jama'a a shekarar 2006.
![]() | ||||
---|---|---|---|---|
Ilé-Ifẹ̀ (yo) | ||||
![]() | ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Osun | |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 501,952 (2003) | |||
• Yawan mutane | 280.26 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 1,791 km² | |||
Altitude (en) ![]() | 280 m | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Jimlar yawan jama'a | |
---|---|
~ 755,260 | |
Yankuna masu yawan jama'a | |
Osun State - 755,260 (2011) · Ife Central: 196,220 · Ife East: 221,340 · Ife South: 157,830 · Ife North: 179,870 |
Bisa al'adar addinin Yarbawa, An kafa 1000 - 800 BC Ilé Ifè bisa ga umarnin abin bauta Olodum are na Obatala. Sai ta fada hannun dan uwansa Oduduwa, wanda ya haifar da gaba a tsakanin su biyun.[2] A can ne Oduduwa ya kafa daular, kuma ‘ya’ya maza da mata na wannan sarki sun zama sarakunan wasu masarautu da dama a kasar Yarbawa.[3] Oòni na farko na Ife ɗan Oduduwa ne, wanda shine Orisha na 401. Mai mulki a yanzu tun 2015 shine Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II, Ooni na Ife wanda kuma akawun Najeriya ne.[4] Birnin na Ife, wanda ake wa lakabi da birnin na gumaka 401, yana da yawan masu bautar wadannan gumakan kuma a nan ne ake gudanar da su ta hanyar bukukuwa.[5]
Birnin Ilé-Ifè ya shahara a duniya saboda kasancewar karfen tagulla, na dutse da terracotta a birnin, tun daga 1200 zuwa 1400 AD [5]