From Wikipedia, the free encyclopedia
Cutar hanta (wadda a da aka fi sani da cutar hanta mai yaɗuwa) wata matsananciyar cuta mai yaɗuwa da ke shafar hanta wadda ƙwayar cutar hepatitis A ke haifarwa (HAV).[1] Yawancin matsalolinta na da ƙarancin bayyana musamman ga ƙananan yara.[2] Lokacin tsakanin kamuwa da kuma bayyana, ga waɗanda suka kamu, na tsakanin mako biyu da mako shida.[3] Idan akwai alamu, yawan cin su kan ɗauki tsawon mako takwas kuma za su iya haɗawa da tashin zuciya, amai, gudawa, fata ta koma launin ɗorawa, zazzaɓi, da ciwon ciki.[2] Kimanin kaso 10–15% na jama'a na haɗuwa da maimaituwar bayyanar alamu a cikin tsawon watanni shida bayan kamuwar farko.[2] Matsanancin hali na gazawar hanta kan afku musamman ga tsofaffi.[2]
Cutar hanta A | |
---|---|
Description (en) | |
Iri |
viral infectious disease (en) , viral hepatitis (en) , waterborne disease (en) cuta |
Specialty (en) | infectious diseases (en) |
Sanadi | Hepatitis A virus (en) |
Symptoms and signs (en) |
Ciwon hanta, nausea (en) , amai, zazzaɓi, malaise (en) , Shawara anorexia (en) |
Disease transmission process (en) | fecal–oral route (en) |
Physical examination (en) |
ELISEA (en) polymerase chain reaction (en) |
Identifier (en) | |
ICD-10 | B15 |
ICD-9 | 070.0 da 070.1 |
DiseasesDB | 5757 |
MedlinePlus | 000278 |
eMedicine | 000278 |
MeSH | D006506 |
Disease Ontology ID | DOID:12549 |
Yawan cin wannan cuta na yaɗuwa ta hanayar cin abinci ko abin sha wanda ya gurɓata da bayan garin da ya harbu.[2] Tafasashshen Kifi wanda bai dahu sosai ba shi ne tushen da aka fi sani.[4] Kuma za'a iya yaɗata ta hanyar cuɗanya ta kusa-da-kusa da mutumin da ya kamu.[2] A yayin da alamomin cutar wasu lokuta ba sa bayyana ga yara ƙanana, za su iya harbar wasu.[2] Bayan kamuwa sau guda, mutum ya sami kariya iya tsawon rayuwarsa.[5] Yin magani na bukatar gwajin jini saboda alamomin cutar sun yi kama da sauran wasu cutuka.[2] Tana daga cikin ƙwayoyin hepatitis: A, B, C, D, and E.
Allurar hepatitis A ta fi inganci wajen kariya.[2][6] Wasu ƙasashe na bayar da shawarar yinta ga ƙananan yara da kuma waɗanda suka fi shiga cikin haɗarin kamuwa da ita waɗanda ba'a yi masu riga-kafi ba a baya.[2][7] Ta na da matuƙar amfani ga rayuwa.[2] Wasu hanyoyin kariya sun haɗa da wanke hannu da kuma dafa abinci sosai.[2] Babu takamaiman jiyya, tare da sauran domin maganin tashin zuciya ko gudawa da aka bayar da shawara domin sha dangane da bukata.[2] Ana iya maganin kamuwa gaba ɗaya kuma ba tare da ci gaban cutar hanta ba.[2] Jiyyar matsananciyar cutar zuciya, idan ta afku, sai dai ta hanayar dashen zuciya.[2]
A duniya gaba ɗaya kimanin mutane miliyan 1.5 cutar ke kamawa a kowace shekara[2][8] Ta fi samuwa a ɓangarorin duniya marasa tsafta da kuma rashin ruwan sha mai tsafta.[7] A ƙasashe masu tasowa kimanin kaso 90% na yara ne su ka kamu daga shekara 10 kuma saboda haka su kan sami kariya lokacin da suka girma.[7] A kan sami ɓarkewarta wasu lokuta a ƙasashe masu tasowa inda yara ba su da kariya lokacin da su ke tasowa kuma babu isasshen riga-kafi.[7] A shekara ta 2010, mummunar cutar hanta ta yi sanadin mutuwar mutane 102,000.[9] Ranar Cutar Hanta ta Duniya a kowace shekara a ranar 28 ga watan Yuli na zama ranar cutar hanta domin wayar da kan jama'a dangane da mummunar cutar ta hanta.[7]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.