![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/8a/Asian_Development_Bank_headquarters.jpg/640px-Asian_Development_Bank_headquarters.jpg&w=640&q=50)
Bankin Cigaban Asiya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Bankin Cigaban Asiya, da turanci The Asian Development Bank (ADB) wani babban bankine dake Asiya an samar dashi ne dan cigaban yankin, An kirkira bankin ne a ranar 19 ga watan Disamba, shekarar alif 1966,[1] Helkwatar bankin na a Ortigas Center dake birnin Mandaluyong, Metro Manila, a kasar Filipin. Har wayau Kamfanin nada Rassa 31 na ofisoshi a ko'ina a duniya[2] Makasudin kafa bankin shine dan a Samar da wata cibiya da zai jagoranci cigaban al'umma da tattalin arziki a tsakanin kasashen Asiya. Daga mambobi 31 a sanda aka kafa kungiyar a yanzu kungiyar nada mambobi 67, a inda 48 suna daga nahiyar ne, sai kuma 19 wadanda ke daga wajen nahiyar. Itama dai bankin ansamar da ita ne akan aiki kusan iri daya data Bankin Duniya, kuma kusan hanya daya suke bi wurin rarraba wakilai, da samar da rahoto da kasafin kudin da akai amfani dasu na wannan shekara. Akwai wani gagarumin tallafi da bankin ke bayarwa a duk shekara ga dalibai 150 dan yin karatu a kasashe 10 dake a nahiyar, Sunan da akafi sanin shirin dashi shine (ADB-Japan Scholarship Program (ADB-JSP) ) a turance, ana da burin bayan daliban sun kammala yin karatunsu, zasu koma kasashen su sutaimaka akan cigaba da bunkasa tattalin arzikin kasar tasu.[3] Bankin yakasance wakili mai sa'ido ga Majalisar Dinkin Duniya Observer.[4]
![]() | |
---|---|
![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Suna a hukumance |
Asian Development Bank |
Gajeren suna | ADB |
Iri |
international financial institution (en) ![]() ![]() ![]() |
Masana'anta |
development aid (en) ![]() |
Ƙasa | Filipin |
Aiki | |
Mamba na |
Committee for the Coordination of Statistical Activities (en) ![]() |
Member count (en) ![]() | 68 (2022) |
Ma'aikata | 3,687 (2022) |
Harshen amfani | Turanci |
Mulki | |
Shugaba |
Masatsugu Asakawa (en) ![]() |
Hedkwata | Mandaluyong |
Financial data | |
Budget (en) ![]() | 819,000,000 $ (2021) |
Assets | 282,100,000,000 $ (2021) |
Net profit (en) ![]() | 730,000,000 $ (2021) |
Stock exchange (en) ![]() |
Australian Stock Exchange (en) ![]() |
Tarihi | |
Ƙirƙira |
19 Disamba 1966 1966 |
Awards received | |
![]() ![]() ![]() ![]() |
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/2/21/Asian_Development_Bank.png/640px-Asian_Development_Bank.png)
tun daga ranar 31 ga watan Disember, shekara ta 2016, kasar Japan da Amurika suna da jari mafi tsoka a bankin, Wanda yakai 15.607%. Sai kasar sin tanada 6.444%, Kasar Indiya nada 6.331%, sannan akarshe kasar Australiya ita kuma keda 5.786% na jari.