Rubutun addinin musulunci na tsakiya From Wikipedia, the free encyclopedia
Al-Qur'ani
Alqur'ani mai girma | ||||
---|---|---|---|---|
Asali | ||||
Shekarar ƙirƙira | 631 | |||
Asalin suna | القرآن | |||
haɗawa a | Makkah da Madinah | |||
Characteristics | ||||
Genre (en) | religious literature (en) da religious text (en) | |||
Harshe | Ingantaccen larabci | |||
Kintato | ||||
Narrative location (en) | Yankin Larabawa | |||
Kallo
| ||||
Chronology (en) | ||||
|
(Larabci: القرآن al-Qur'an), ko kuma Alƙur'ani mai girma kamar yanda akasani, shine littafin da Allah ya saukar a harshen Annabin Rahama, wato Larabci, kuma shine littafin da Allah ya rufe saukar da duk wani littafi mai tsarki a bayansa, (babu littafin da Allah zai sake saukarwa a bayansa) kamar yadda Allah ya saukar ga Annabawan da suka gabata, domin Annabi Muhammadu shine cika makin Annabawan Allah.
Wanda Allah ya saukar da ayoyinsa ga Annabin musulunci Annabi Muhammad (S.A.W) ta hannun mala'ika Jibrilu. A cikin aƙidar Musulunci, Ƙur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma mafi girman mu'ujizar Annabi Muhammad (S.A.W), yana tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S.A.W) Manzone na gaskiya.[1]
Shari'ar Musulunci, wacce kuma ake kira sharia, ta dogara ne akan Ƙur'ani (Madogararsa na Farko), shine littafin da musulmai suke karantawa, kuma suke aiki dashi, tare da hadisai Waɗanda suke sune maganar da fito daga harshen Annabi Muhammad. Musulmai suna karanta ayoyin kur'ani daban-daban a cikin addu'o'insu.
Lafiyayyan hankali da tsaftataccen tunani na ɗan Adam da ayyuka na yau da kullum sun tabbatar da cewa kur'ani ya bada cikakkiyar kulawa da kariya ta fuskar haƙƙin ɗan adam na duniya, da 'yancin ɗan adam.[2]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.