![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/1/12/Aba_Nigeria_hotel.jpg/640px-Aba_Nigeria_hotel.jpg&w=640&q=50)
Aba
From Wikipedia, the free encyclopedia
Aba birni ne, da ke a jihar Abia, kudu-maso-gabashin Najeriya, kuma itace cibiyar kasuwanci na jihar Abia. A yayinda aka samar da jihar Abia a shekara ta 1991, An raba Aba zuwa kananan hukumomi biyu; Aba ta kudu da kuma Aba ta yamma. Aba ta kudu itace mafi muhimmanci kuma itace cibiyar Jihar Abiya. Birnin tana nan a gabar kogin Aba. Aba tana da kauyuka kaman su Aba-Ukwu, Eziukwu-Aba, Obuda-Aba, Umuokpoji-Aba da makamantansu. Kabilar "Ngwa" na iyamuaran Najeriya suka samar da jihar Aba a matsayin kasuwa daga bisani kuma turawa suka gina barikin sojoji a birnin a 1901.[1] Tana daga yammacin yankin kogin Aba, kuma tana daura da titin zuwa jihar Portharcourt, Owerri, Umuahia, Ikot Ekpene, da kuma Ikot-Abasi.[2] Birnin Ta zamo wajen tattara kayan amfanin gona bayan turawa sun samar da titin jirgin kasa wanda ya ratse birnin zuwa birnin Portharcourt. Aba ta kasance birni kuma cibiyar kasuwanci a yanki mai zagaye da kananan kauyuka da birane.
![]() | ||||
---|---|---|---|---|
![]() | ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Abiya | |||
Ƙaramar hukuma a Nijeriya | Aba ta Kudu | |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 1,160,000 (2022) | |||
• Yawan mutane | 16,111.11 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 72 km² | |||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Aba River (Nigeria) | |||
Altitude (en) ![]() | 205 m | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Lambar aika saƙo | 450 | |||
Kasancewa a yanki na lokaci | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | 082 | |||
Wasu abun | ||||
| ||||
Yanar gizo | abiastate.gov.ng |
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/7/79/ABA_MAIN_PARK.jpg/640px-ABA_MAIN_PARK.jpg)
Asalin mutanen Aba sune kabilar Ngwa. Sannan Aba tayi fice ta fuskar kwararrun 'yan siyasa dake cikinta kuma itace birnin da tafi kowace birni tara yawan jama'a a yankin kudu maso gabashin. An ayyana cewa Aba tana da yawan mutane kumanin 2,534,265 a 2016.[3]