From Wikipedia, the free encyclopedia
Youssouf Togoïmi (an haifeshi ranar 26 ga watan Maris, 1953 - ya mutu ranar 24 ga Satumban shekarar 2002 ) ɗan siyasan ƙasar Chadi ne wanda ya yi aiki a cikin gwamnati a ƙarƙashin Shugaba Idriss Déby amma daga baya ya jagoranci wata ƙungiyar tawaye, the Movement for Democracy and Justice in Chad (MDJT), a kan Déby.
Youssouf Togoïmi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 26 ga Maris, 1953 |
ƙasa | Cadi |
Mutuwa | 24 Satumba 2002 |
Karatu | |
Harsuna |
Larabci Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
An haife shi a garin Zouar a cikin tsaunukan Tibesti, ya fito ne daga arewacin musulmin ƙasar. Togoïmi ya yi aiki a mukamai da yawa a lokacin shugabancin Idriss Déby: ya kasance Ministan Shari'a daga shekarar 1990 zuwa 1993, Ministan Tsaro daga shekarar 1995 zuwa 1997, sannan kuma aka nada shi Ministan cikin gida a ranar 21 ga Mayun 1997. [1] Jim kaɗan bayan nadin na ƙarshe, ya yi murabus daga mukaminsa na gwamnati a ranar 3 ga watan Yunin 1997. Ya ce murabus din nasa ya samo asali ne saboda abin da ya bayyana da "mulkin kama-karya" ta gwamnati. Hakanan an fassara barin aikin da Togoïmi yayi da Déby a matsayin abin da ke da alaƙa da ƙabilanci dangane da kasantuwar sa ɗan ƙabilar Toubou shi kuma Déby ɗan ƙabilar Zaghawa.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.