From Wikipedia, the free encyclopedia
Sallar Zuhur ( Larabci: صَلَاة ٱلظُّهْر ) tana ɗaya daga cikin sallolin Musulunci na farilla ( sallah ). Ana yin ta ne bayan sallar asuba da kuma gabanin sallar la'asar, tsakanin gushewar rana daga tsakiya shine zaɓaɓɓen lokacin ta zuwa kusa da lokacin La'asar tana zamowa laluri ne zuwa faɗuwar rana.[1]
Sallah Azzahar | |
---|---|
Sallah | |
Bayanai | |
Mabiyi | Sallan Alfijiri |
Ta biyo baya | Sallar la`asar |
A ranar Juma’a ana maye gurbin Sallar Azahar da sallar Juma’a wadda wajibi ce ga maza Musulmi waɗanda suka wuce shekarun balaga kuma suke baligai masu hankali da lafiya su yi salla a cikin jam’i ko dai a masallacin Jumu'a ko kuma dai ga waɗanda basu samu sallar juma'a ba, Sai suyi Sallah Azahar raka'a huɗu kenan cif.[ ]
Khutbah (wa'azi) liman ne yake gabatar da ta, a ranar juma'a.
Kuma ana kiranta da Zuhr, Duhr, Thuhr ko Luhar.
Salloli biyar a dunkule guda ɗaya ne na rukunnan Musulunci guda biyar, a cikin Musuluncin Sunna, kuma ɗaya daga cikin rukunan Imani.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.