From Wikipedia, the free encyclopedia
Jalāl ad-Dīn Muhammad Rūmī (جلالالدین محمد رومی), akan kirasa da Jalāl ad-Dīn Muhammad Balkhī (جلالالدین محمد بلخى), Mevlânâ/Mawlānā, (مولانا, "our master"), Mevlevî/Mawlawī (مولوی, "my master"), ko kuma kawai Rumi (haihuwa 30 ga watan Satumba 1207 – rasuwa 17 ga watan Disamba 1273), mutumin ƙarni na 13th ne, daga ƙasar Persian.[1][2] Ya kasance fitacce kuma shahararren mawaƙi, mai shari'a, malamin musulunci, mai Koyar da Addini, kuma sufi mystic asalin sa daga Greater Khorasan yake.[2][3] ɗaukakar Rumi ta tsallaka zuwa ƙasashe da ƙabilu daban daban, ciki da wajen Iran, Tajiks, Turkawa, Greeks, Pashtuns, wasu Central Asian Muslims, da kuma musulman Kudancin Asiya suna matukar yarda da shi akan aikinsa ga tsaftacen zukata tun a tsawon karnuka bakwai dasuka gabata.[4] Wakensa an fassarasu zuwa yarukan duniya daban daban da kuma sake rerasu zuwa nau'uka daban daban. Rumi dai an kamanta shi a matsayin "Mafi Shaharar Mawaki"[5] kuma "Mawakin da aka fi sayensa" a ƙasar Amurka.[6][7]
Rumi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Vakhsh (en) , 30 Satumba 1207 (Gregorian) |
Harshen uwa | Farisawa |
Mutuwa | Konya, 17 Disamba 1273 (Gregorian) |
Makwanci |
Mevlâna Museum (en) Yeşil Türbe (en) |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Baha ud-Din Walad |
Abokiyar zama | Gawhar Khatun (en) |
Yara | |
Karatu | |
Harsuna |
Farisawa Larabci Old Anatolian Turkish (en) Medieval Greek (en) |
Malamai |
Baha ud-Din Walad (en) Burhanuddin Tirmizi (en) |
Ɗalibai | |
Sana'a | |
Sana'a | maiwaƙe, Ulama'u, marubuci, literary (en) , mai falsafa da mystic (en) |
Muhimman ayyuka |
Seven Sessions (en) Fihi Ma Fihi (en) Masnavi (en) Diwan-e Shams-e Tabrizi (en) Maktubat (en) |
Wanda ya ja hankalinsa | Shams Tabrizi (en) , Ibn ul-Arabi da Abdulƙadir Gilani |
Sunan mahaifi | خاموش |
Imani | |
Addini |
Musulunci Sufiyya |
Yawancin ayyukan Rumi yayi sune a harshen Persian, amma wasu lokuta yana amfani da Turkish, Arabic, da kuma Greek,[8][9][10] a wata ayarsa.[11][12] na Masnavi (Mathnawi), wanda aka haɗa a Konya, ana ganin tana ɗaya daga cikin daukakan waka a harshen Farisa.[13][14] Ana karanta ayyukansa a ko ina a asalin harshen daya rubutasu har ayau tsakanin Greater Iran da ƙasashen dake amfani da harshen Farisa.[15][16] Fassarorin ayyukan sa sun shahara a ƙasar Turkiya, Azerbaijan, da Amurika, da kuma kudancin Asiya.[17] waqen sa sun taimaka sosai bawai kawai a Persian literature, dai dama Turkish, Ottoman Turkish, Azerbaijani, da kuma wasu literature na wasu Turkic, Iranian, da Indo-Aryan languages wanda ya haɗa da Chagatai, Urdu da Pashto.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.