From Wikipedia, the free encyclopedia
Raƙumi dai wata halitta ce daga cikin dabbobin da Allah maɗaukakin Sarki ya halitta bisa hikima da ikonsa. Babu shakka akwai ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da Allah ya keɓanci raƙumi da su. Kuma ya halicci raƙumi da su ne, domin su zamo ayoyi abin lura ga ma'abota hankali.
Raƙumi | |
---|---|
Scientific classification | |
Class | mammal (en) |
Order | Artiodactyla (en) |
Dangi | Camelidae (en) |
genus (en) | Camelus Linnaeus, 1758
|
Geographic distribution | |
Kasancewa akwai zafi mai tsananin gaske a hamada, wanda ba duka halittu za su iya jurewa ba. Sannan kuma akwai ƙura haɗe da yashi da take tashi koda yaushe, wadda take rufe duk wata halitta da ta ci karo da ita. Ga babbar halitta kuma ƙurar takan sa wahalar nunfashi da shaƙar iska. Idan ka ɗauke ƙananan halittu dangin su kadangare, raƙumi shi ne kaɗai wata ƙatuwar halitta da take iya rayuwa a cikin hamada. Kuma mahaliccin raƙumi ya halicce shi ne musamman domin ya rayu a cikin hamada, ya kuma zama mai hidima ga al'ummar dake rayuwa a wannan ɓangare.
Abu mafi muhimmanci da aka fi buƙata a hamada shi ne ruwa, domin a yi maganin ƙishirwa, amma kuma abu ne mai wahalar gaske a samu ruwa a hamada. Kuma ba abu ne mai yiwuwa ba, a samu wani abinci a cikin yashin hamada. Hakan na nufin kenan duk wata dabba da za ta rayu a hamada, ya zama wajibi ta zamanto tana da wata kariya daga jin ƙishirwa da kuma yunwa. Babu shakka haka abin yake ga raƙumi, domin babu wata dabba da ta fi shi jure ƙishirwa da yunwa.
Raƙumi zai iya rayuwa har na tsawon kwana takwas ba tare da ci ko sha ba. Don haka kum, idan raƙumi ya samu inda zai sha ruwa, kasancewar yana da matuƙar buƙatarsa, sai ya sha ya kuma ajiye wani ruwan a cikinsa. Raƙumi yakan iya shan ruwan da kuma ya kai ɗaya bisa uku na girmansa a cikin minti goma kacal, wato kwatankwacin galan 30 kenan.
Tozon raƙumi kuwa na tattare da kitsen da ya kai kilo 40. Godiya ta tabbata ga wanda ya halicci tozon raƙumi, yadda zai sa raƙumi ya yi kwanan da kwanaki a cikin hamada ba tare da cin abinci ba.
Mafiya yawan dangogin abinci da ake samu a hamada busassu ne, kuma masu tauri, amma duk da haka, an tsara halittar kayan cikin raƙumi yadda za su iya narkar da kusan duk wasu nau'o'in abinci da ake samu a hamada, komai taurinsa kuwa. Mahaliccin rakumi ya halittar masa waɗansu irin haƙora yadda za su dace da abincinsa.
Babu shakka ƙurar hamada na daga cikin gararin da halittun da ke ratsa hamada ke fama da ita, saboda tana shigar masu ido, ta kuma hana su shaƙar iska yadda ya kamata. Amma mahaliccin raƙumi ya halitta masa wata fata daga saman idonsa kamar gilashi, wadda take sakkowa yayin da iskar hamada ta taso, sai ta zama kariya ga idon. Sannan ga kuma dogon gashin ido mai kauri da yake hana tsakuwoyin yashin hamada isa ga idon raƙumin.
Har ila yau, an tsara halittar hancin raƙumi yadda idan iska mai yashi ta taso zai iya manne ƙofofin hancinsa, ya riƙa shaƙar iska ta wata ‘yar kafa ta musamman mai cike da kariya, yadda babu wani yashin hamada da zai shiga cikinsa.
Ɗaya daga cikin matsalolin da abubuwan hawa ke fuskanta yayin ratsa hamada shi ne kafewa a cikin yashi. Amma irin wannan haɗari bai taɓa faruwa ga raƙumi ba, koda kuwa yana ɗauke da labtun kaya, saboda an kuma halicci ƙafafuwan raƙumi ne musamman saboda ratsa hamada. Kasancewar kofaton raƙumi yana da wani maganaɗisu da baya barinsa ya kafe cikin yashi, saboda kofaton yana aiki ne kamar takalmin da Bature yake amfani da shi idan zai ratsa ta cikin dusar ƙanƙara. Sannan kuma doguwar ƙafarsa ta nisanta shi da tiririn zafin yashin hamada.
Jikinsa kuma na rufe shi da wata fata ta musamman, wadda take iya kare shi daga zafin rana ko kuma zafin yashi a lokacin da yake kwance. Wanna tsari na halittar raƙumi, shi ne abin da ya fito da halittar raƙumi fili, a matsayin wata cikakkiyar halitta.
Bari mu yi wa mai karatu wata tunatarwa ta musamman dangane da ɓangarorin halittar raƙumi da muka bayyana;
Saboda haka kuma waɗannan gaɓoɓi na raƙumi da ma sauran da ba mu iya ambaton su anan ba, suna nusar da mu ne ga wata hujja tabbatacciya. Wato dai raƙumi wata ƙasaitacciyar dabbace da mahalicci ya halitta domin ya iya biyan buƙatar al'ummar da suke rayuwa a ɓangaren hamada. Wannan mahalicci kuwa shi ne Allah maɗaukaki kuma mahaliccin komai.
Rakumi dabbace Mai dogon tarihi a fadin duniya, rakumi tana daga cikin dabbobi masu daraja a cikin duniya, sannan rakumi na daya daga cikin dabbobi wanda suke jure wahala sosai fiye da mafi yawan dabbobi. Akanyi anfani da fitsarin rakumi wajen yin magani, har ila yau Ana sayarda fitsarin rakumi, wasu daga cikin mutane sun Mai da sayar da fitsarin rakumi tamkar sana'ar su kasan cewar fitsarin rakumi tana maganin cutartuka da dama a jikin mutum, sannan rakumi yana daya daga cikin dabbobi masu tsada a duniya. Rakumi yana daga cikin dabbobin da akafi yawan gani a gidan zoo kuma daya daga cikin dabbobin da akafi sani a duniya. Santtp://www.dw-world.de/dw/article/0,,3880536,00.html Tsawon kwanaki nawa raƙumi yake iya yi ba tare da ci ko sha ba]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.