Matan Annabi sha uku From Wikipedia, the free encyclopedia
Matan Annabi Ta tabbata a cikin nassoshi cewa Annabi Muhammad (S A W) ya aura mata 11 a tsawon rayuwarsa sai dai wasu ruwayoyin sun nuna matansa 13. A Musulunce da kuma duk wani Musulmin kwarai na gari ana kiran su da Ummahati al-Muminin (Larabci: أم ٱلْمُؤْمِنِين; ma'ana 'Uwar Muminai'/Iyayen muminai) ana ambaton su da wannan kalma a matsayin alamar girmamawa, wannan kalmar ta samo asali daga Alqur'ani yazo a cikin Suratul Ahzaab {{النَّبِيُّ أَوْلَى بِالْمُؤْمِنِينَ مِنْ أَنْفُسِهِمْ وَأَزْوَاجُهُ أُمَّهَاتُهُمْ وَأُولُو الْأَرْحَامِ بَعْضُهُمْ أَوْلَى بِبَعْضٍ فِي كِتَابِ اللَّهِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُهَاجِرِينَ إِلَّا أَنْ تَفْعَلُوا إِلَى أَوْلِيَائِكُمْ مَعْرُوفًا كَانَ ذَلِكَ فِي الْكِتَابِ مَسْطُورًا Aya-6.png}} haka kuma Allah madaukakin sarki yana cewa a cikin Alqur'ani { ﴿يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا ٣٢﴾ [الأحزاب:32.[1][2]
Matan Annabi | |
---|---|
group of humans (en) | |
Bayanai | |
Bangare na | Ahl ul-Bayt |
Depicts (en) | Mata a musulunchi, women in the Qur'an (en) da female figures in the Quran (en) |
Alaƙanta da | Yaran Annabi |
Annabi Muhammad (S A W) ya auri matarsa ta farko, a lokacin da yake da shekara 25 wato Nana Khadija bint Khuwaylid Allah ya kara mata yarda. Sun zauna da ita tsawon shekaru 25 har sai da Allah ya mata rasuwa. Bayan mutuwarta a cikin shekara 619 AD, ya auri mata 10 a cikin sauran shekarun rayuwarsa. Daga cikin wadannan matan biyu suka haifa masa ‘ya’ya: Nana Khadijah da Nana Mariya al-Qibtiyya Allah ya kara yarda da su. Duk matan Annabi sun kasance zawarawa kodai wadda aka saka ko kuma wadda mijinta ya mutu, ban da Aisha bint Abubakar Allah ya kara mata yarda. Baban ta Abubakar bin Abi Quhafa shine Khalifah na farko bayan rasuwar Annabi Muhammad (S A W)
Rayuwar Annabi Muhammad ta kebanta da zamani guda biyu: Makka kafin hijira, birni ne a yammacin kasashen Larabawa, daga shekara ta 570 zuwa 622 Miladiyya, da kuma bayan hijira a Madina, daga 622 har zuwa rasuwarsa a shekara ta 632. Hijira tana nuni ne ga yawan hijirar Fiyayyen halitta Annabi Muhammad da Sahabbansa, wanda akwai hijira ta farko da ta biyu, ta farko itace wadda ysa umurci Sahabbansa da suyi hijira zuwa garin Habasha, sai ta biyu sun tafi garin Madina tareda da abokin sa Abubakar saboda zalunci da musulmi suka fuskanta daga kafiran Makka na wannan lokacin. Bayan wannan hijirar duk an daura aurensa sai biyu.
Annabi Muhammad (S A W) ya zauna da iyalansa a wasu kananan gidaje kusa da masallacin Madina. Kowanne daga cikin waɗannan gidaje ya kasance faɗinsa mita shida zuwa bakwai, sai kuma da tsayi goma (mita 2.3). Tsayin rufin ya kasance na wani matsakaicin mutum a tsaye. An yi amfani da barguna a matsayin labule don rufe kofofin. Kamar yadda aka ruwaito daga Anas bin Malik cewa: “Annabi ya kasance yana ziyartar matansa duka wato yana kewayawa su duka, dare da rana, kuma su goma sha daya ne. Na tambayi Anas, "Shin Annabi da ƙarfinsa ne?" Anas ya ce: “Mun kasance muna cewa an bai wa Annabi qarfin mutum talatin (maza). Kuma Sa’id ya ce daga Qatada cewa Anas ya ba shi labarin mata tara ya aura (ba goma sha xaya ba).
Duk da cewa matan Annabi (S A W) suna da matsayi na musamman a matsayin su na Uwayen Muminai, amma bai bar su su yi amfani da matsayinsa na Annabi ba wajen samun kulawa ta musamman a bainar jama’a.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.