From Wikipedia, the free encyclopedia
Babban Masallacin Makkah (da larabci; ٱلْـمَـسْـجِـد ٱلْـحَـرَام a furucci; al-Masjid al-Ḥarām a ilimance; Masallaci mai Tsarki, da turanci; The Sacred Mosque)[1]) shine masallacin daya zagaye Kaaba dake birnin Mecca, Saudiya. Wuri ne na ziyara domin aikin hajji, wanda kowane Musulmi dole ya aikata shi, karanci sau daya a rayuwarsa idan yana da ikon zuwa, wanda aikin yahada da kewaye dakin Kaaba dake a cikin masallacin. Kuma nan muhimmin wurin yin ‘Umrah, karamin aikin hajji da akeyi a kowane lokaci a cikin shekara. Babban masallacin yahada da wasu mahimman wurare, wadanda suka hada da, Baƙin Dutse, Rijiyar ZamZam, wurin tsayuwar annabi Ibrahim, da duwatsun Safa da Marwa.[2] A bude Masallacin yake, akowane lokaci da yanayi.
Masjid al-Haram | |
---|---|
المسجد الحرام | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Saudi Arebiya |
Province of Saudi Arabia (en) | yankin Makka |
Tourist attraction (en) | Makkah |
Coordinates | 21°25′21″N 39°49′34″E |
History and use | |
Grand Mosque Seizure | |
| |
Aikin Hajji | |
| |
Umrah | |
| |
Start of construction | 630 |
Addini | Musulunci |
Maximum capacity (en) | 820,000 |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) | Islamic architecture (en) |
Tsawo | 137.5 m |
Parts | Hasumiya: 9 |
Offical website | |
|
Babban Masallacin harami shine masallaci mafi girma a duniya, kuma anmasa gyararraki da faɗaɗa shi a lokuta daban-daban a shekaru.[3] Ta wuce lokuta da dama ƙarƙashin kulawar Halifofi daban-daban, sultans da sarakuna, kuma ayanzu babban masallacin na ƙarƙashin kulawar Sarkin Saudi Arabia wanda shine Custodian of the Two Holy Mosques.[4] Tana nan ne a gaban Abraj Al Bait, mafi tsayin ginin agogo a duniya,[5] aikin gininsa dake cike da cece-kuce akan rushe wuraren tarihi na farkon musulunci da gwamnatin Saudiya tayi.[6]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.