From Wikipedia, the free encyclopedia
Kannywood ko kuma Hausa Sinima, Itace masana'antar fina-finai na Harshen Hausa da ke a arewacin Najeriya. Cibiyarta na nan a cikin birnin Kano da kuma sauran wasu jahohin Najeriya kamar irin su Jos, Kaduna, Katsina da sauransu.
Kannywood | |
---|---|
film genre (en) da cinema by country or region (en) | |
Bayanai | |
Bangare na | Nollywood |
Suna saboda | Kano da sinimar Amurka |
Nahiya | Afirka |
Language used (en) | Hausa |
Kannywood sunan aro ne dake nufin sinima a harshen Hausa. Wani ɓangare nena babbar siniman Najeriya mai suna Nollywood, wanda ya ƙunshi sauran cibiyoyin shirya fina-finai na harsunan Najeriya da dama. Sunan "Kannywood" kalma ce da aka ƙirƙira daga kalmomi biyu; Kano da Hollywood - kamar dai cibiyar Fina-finan Ƙasar Amurka Hollywood."Kannywood" ta samo asali ne daga ƙarshen shekarar, alif Ɗari tara da casa'in da tara 1990, lokacin da Sanusi Shehu na Mujallar Tauraruwa ya ƙirƙiri kalmar Kannywood sannan kalma tayi fice a matsayi sunan da ake kiran masana'antar a Arewacin Najeriya. An ƙirƙiri kalmar "Kannywood" a shekara ta, 1999, shekaru uku kafin ƙirƙiran kalmar Nollywood.[1]
Marubuta Waƙoƙi da mawaƙa waɗanda ke shirya ko yin waƙa a finafinan Hausa sun haɗa da Nazifi Asnanic,[2][3] Naziru M Ahmad,[4] Ali Jita,[5][6] da Fati Nijar.[7][8] Umar M Shareef.[9].
A shekara ta, 2003, tare da sanuwar kungiyar Izala da kuma hawa karagar mulki na Ibrahim Shekarau, gwamnatin masu tsananin kishin addini na Kano ta fara wani kamfe na nuna adawa ga masana'antar ta Kannywood. Yawancin fina-finai da ake ganin ba sa bin tsarin na addini, an tantance su kuma an daure wasu masu shirya su. Wannan ya jawo cikas ga nasarorin da Kannywood ta samu kuma ya ba masana'antar fim ta Kudancin Najeriya damar samun nasarori fiye da ita.
A cikin shekara ta, 2007, tsiraicin Hiyana : lokacin da faifan batsa na wata fitacciyar 'yar fim ya fito fili ya haifar da mummunan martani daga gwamnatin Islama ta wancan lokacin ta Jihar Kano a ƙarƙashin gwamnatin Mallam Ibrahim Shekarau. Ibrahim Shekarau ya naɗa Babban Darakta a hukumar tace fina-finai, Abubakar Rabo Abdulkareem tare da goyon bayan ƙungiyar Izala da sauran ƙungiyoyin masu kishin Islama, an tantance Fina-finan Kannywood da wasu shahararrun masana'antun littattafan soyayya na harshen Hausa, an kuma daure jaruman fim, marubuta da dai sauransu, sannan Gwamna da kansa ya ƙone Sauran kayan aikin shirye-shirye.[10] A shekara ta, 2011, maye gurbin gwamnatin Islama da mafi sassaucin gwamnati ƙarƙashin jagorancin PDP ya haifar da kyakkyawan yanayi ga masana'antar. A shekara ta,2019, biyo bayan sake zaɓen gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano, hukumar kula da takunkumi ƙarƙashin Sakataren zartarwa, Isma'il Na'abba Afakallahu ta ƙaddamar da wani sabon kamun na maƙada da 'yan fim. An kama wani daraktan fim din, Sanusi Oscar, da wani mawaƙi, Naziru M. Ahmad tare da kai su kotu kan zargin da ake musu na cewa sun saki waƙoƙi ba tare da izinin mai bincike ba. An bayar da belin mutanen biyu(2).[11] Ƙungiyar adawar ta Kwankwasiyya ta bayyana cewa kamun na da nasaba da siyasa saboda ana ɗaukar waɗanda ake zargin a matsayin masu nuna goyon bayan Jam’iyyar ta PDP a zaɓen da ya gabata.[12].
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.