From Wikipedia, the free encyclopedia
Jihadin Islama a Masar (EIJ), [1] [2] asalin sunansa al-Jihad, [3] [4] ƙungiya ce ta 'ƴan ta'adda a Masar bisa tushen wuce gona da kuma iri na fassarar Islama. Tana kuma aiki tun a ƙarshen shekarun 1970. Tana ƙarƙashin takunkumin duniya da Majalisar Dinkin Duniya a matsayin ƙungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda. [5] Haka nan gwamnatoci da yawa a duniya sun dakatar da shi, gami da na Tarayyar Rasha . [6]
Jihadin Islama a Masar | |
---|---|
Bayanai | |
Gajeren suna | EIJ |
Iri | armed organization (en) da terrorist organization (en) |
Ƙasa | Misra |
Ideology (en) | Islamism (en) |
Mulki | |
Shugaba | Ayman al-Zawahiri (en) da Muhammad abd-al-Salam Faraj (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1979 |
Wanda ya samar |
Muhammad abd-al-Salam Faraj (en) Ayman al-Zawahiri (en) Aboud El Zomor (en) Sayyed Imam Al-Sharif (en) Nabil Na'eem (en) |
Dissolved | ga Yuni, 2001 |
Tun 1991 ta ke jagorancin Ayman al-Zawahiri, wanda yanzu shi ne shugaban kungiyar al-Qaeda. A cewar Zawahiri, EIJ "ya kuma banbanta da kungiyar Takfir wal Hijra saboda ba ma daukar mutane kafirai saboda zunubansu. Kuma mun sha bamban da kungiyar ‘Yan'uwa Musulmi saboda wani lokacin ba sa adawa da gwamnati”. [7]
Babban burin ƙungiyar shi ne asalin kifar da gwamnatin Masar tare da maye gurbinta da ƙasar musulinci bisa tsarin da take tunanin yakamata musulinci ya kasance. Daga baya ta faɗaɗa manufofinta waɗanda kuma suka haɗa da kai wa Amurka da Isra'ila hari, da sauran muradun Misira da ƙasashen waje.
Jihadin Islama ne ke da alhakin kisan Anwar Sadat a 1981. Yarjejeniyar Sadat da Sinai da Isra’ila, wacce ta amince da mulkin Yahudawa, ya ba su haushi sosai. [4]
A watan Yunin 2001, Al Qaeda da Jihadin Islama na Masar, wadanda suke da alaƙa da juna tsawon shekaru, suka hade cikin 'Qaeda al-Jihad'.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.