Remove ads
Jami'ar Najeriya dake kalabar jihar Cross River From Wikipedia, the free encyclopedia
Jami'ar Calabar jami'a ce ta jama'a da ke Calabar, Jihar Cross River, Najeriya. Tana ɗaya daga cikin jami'o'in gwamnatin tarayya na zamani.[1] Jami'ar Calabar ta kasance a harabar Jami'ar Najeriya har zuwa shekara ta 1975.[2] Mataimakiyar shugabar jami'ar ita ce Florence B. Obi. Matsayin DVC (Academic) yana hannun Angela Oyo Ita, yayin da Grace Eno Nta, ita ce DVC (Administration).[3]
Jami'ar Calabar | |
---|---|
| |
Knowledge for Service | |
Bayanai | |
Suna a hukumance |
University of Calabar |
Iri | jami'a |
Ƙasa | Najeriya |
Laƙabi | Maalabites |
Aiki | |
Mamba na | African Library and Information Associations and Institutions (en) da Ƙungiyar Jami'in Afrika |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1975 |
|
John Elliott ne ya tsara gine-ginen jami'ar.[ana buƙatar hujja] An kafa ta ne bisa doka don cika wannan umarni na gargajiya, taken jami'ar shi ne, "Ilimi don yin Hidima".[4]
Jami'ar Calabar ta kasance ɗaya daga cikin manyan Jami'o'in Najeriya don sarrafa tsarin yin rajistar dalibai ta hanyar Kwalejin,[5] kuma ta ɗauki mataki na gaba don daidaita dangantakar tsoffin ɗalibanta wanda ya haɗa da buƙatar kwafin yanar gizo da sarrafa na farko irinsa a cikin ƙasa.[6]
Ɗakin karatu na, University of Calabar Library da aka sani da Definitive Library an kafa shi a 1975.[7] ɗakin karatun yana da wurin zama na masu karatu dubu 3000, ofisoshin ma'aikata 16 da ke tallafawa koyarwa, bincike da ayyukan al'umma. An yi shirin aje litattafai sama da miliyan ɗaya tare da fadin murabba'in mita 22,746 na girman ɗakin karatun.[8]
Manyan shugabannin jami’ar a halin yanzu da muƙamansu kamar haka.
Ofishin | Masu riƙewa |
---|---|
Baƙo | Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari |
Chancellor | Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero |
Pro-Chancellor & Shugaban Majalisar | Gen. (rtd) Martin Luther Agwai |
Mataimakin shugaban jami'a | Farfesa Florence Obi |
Mataimakin Mataimakin Shugaban Jami'ar (Malamai) | Farfesa Angela Oyo-Ita |
Mataimakin Shugaban Jami'ar (Administration) | Farfesa Eno Grace Nta |
Ma'aikacin Laburaren Jami'a | Farfesa Aniebiet Inyang Ntui |
Magatakarda | Malam Gabriel O. Egbe |
Bursar | Mr. Aniefiok Godwin Williams |
Jami'ar tana da Sassa masu zuwa:
Wannan jerin cibiyoyin haɗin gwiwa ne na Jami'ar Calabar da Hukumar Kula da Jami'o'i ta ƙasa (NUC) ta sahale mata.[10]
Daga cikin tsofaffin ɗaliban Jami'ar Calabar akwai:
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.