Ethiopian Airlines
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Ethiopian Airlines (EAL) kamfanin sufurin jirgin sama ne mai mazauni a birnin Addis Abeba, a ƙasar Habasha,[1][2] kuma kamfanin ya kasance mallakin gwamnatin kasar. An kafa kamfanin a ranar 21 ga watan Disemban 1945 kuma ya fara aiki a a ranar 8 ga watan Aprelun 1946, sannan ya fadada zuwa sufuri tsakanin kasa da kasa a shekarar 1951. Kamfanin ta fara ba da hannun jari a shekarar 1965 kuma an sauya masa suna daga Ethiopian Air Lines zuwa Ethiopian Airlines.
Remove ads






Filin jirgin saman ya kasance memba na International Air Transport Association tun daga 1959 da kuma Kungiyar Filayen Jirgin Sama na Afurka a 1968. Kamfanin memba ne na Star Alliance, tun lokacin da suka shiga kungiyar a cikin watan Disemban shekara ta 2011. Inkiyar filin jirgin itace 'New Spirit of Africa' Ethiopian's hub,[3] kuma hedikwatar ta na nan a Filin jirgin saman Addis Abeba, a babban birnin Addis Ababa, inda take sufurin fasinjoji 125 - 20 daga cikinsu a tsakanin kasa, 44 kuma jigilar kayayyaki. Filin jirgin yana da manyan rassa a Togo da Malawi.[4] Filin jirgin ta Ethiopia itace mafi girma a Afurka ta fuskar jigilar fasinjoji, wuraren sauka, girman jirage da kuma kudaden shiga.[5][6] Filin jirgin har wayau shine na hudu a duniya dangane da yawa wuraren sauka a fadin duniya.[7]
Yana da jiragen sama 117, daga kamfanonin Airbus, Boeing da De Havilland Canada.[8]
Remove ads
Tarihi
1940s: Da farko
Bayan samun yancin kan kasar habasha wato Ethopia, Mai daraja Haile Selassie I ya nemi taimakon Amurka, Burtaniya da faransa akan su taimake shi ya gina babban kamfanin jirgin sama a matsayin sabon cigaban da zai iya samam al'ummar kasar shi[9] Awani rahoto da BBC suka fitar sun yayi wannan yunkuri ne na gina babban kamfanin jirgin sama a kasar domin tsame kasar daga halin talauci[10] A cikin shekarar 1945, Gwamatin Ethopia ta fara hadin gwaiwa da kamfanonin manyan jiragen sama. A ranar 8 ga watan 1945, TWA ta rattaba hannu a yarjejeniya [11]
Remove ads
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads