From Wikipedia, the free encyclopedia
Enugu ta Kudu karamar hukuma ce dake a jihar Enugu kudu maso Gabashin Nijeriya. Hedikwatan Ƙaramar hukumar na yankin Uwani,[1] kuma karamar hukumar ta kunshi gundumomi kamar haka; Akwuke, Amechi, Ugwuaji, Obeagu, Awkunanaw da kuma Amechi-Uwani. Karamar hukumar Enugu ta Kudu ta hada yankin da Enugu ta Arewa daga arewa, sannan kuma daga gabas da karamar hukumar Nkanku (East) ta Gabas.
Enugu ta Kudu | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jiha | Jihar Enugu | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 67 km² |
Tana da faɗin kasa aƙalla 67 kmsq,[2] da yawan mutane kimanin mutum 198,723 a cikin ta, dangane da ƙidayar shekara ta 2006, sannan an ayyana yawan mutane garin a shekara ta 2016 a matsayin kimanin mutum 267,300.[3] Mafi akasarin mutanen karamar hukumar Inyamurai ne a dalilin haka Igbonci/Inyamuranci da turanci ne harsunan da aka fi amfani dasu a Enugu ta Kudu.[2] Lambobin tura saƙonni zuwa yankin su ne 400.[4]
Enugu ta kudu ta mamaye fili mai fadin 67kmsq na jihar kuma tana da matsakaicin yanayi na zafi/sanyi na kimanin 27degrees centigrade. Yankin na fuskantar yanayi na damshi na kimanin kaso 69% kuma akwai yanayi biyu a yankin; lokacin rani da kuma lokacin damuna da kuma gajerar lokaci na sanyi a shekara.[2] Sanannun wurare a yankin sun hada da; wurin siyayyar "Roban stores shopping Mall" dake hanyar Agbani (road), kwalijin "Holy Rosary College" da kuma wurin hutu na "Ngwo relaxation park".
Karamar hukumar Enugu ta kudu tana da tarin arzikin ma'adanan coal (kamar dai Birnin Enugu) sannan tana daga cikin yankin da ake kira da "Birnin gawayin-coal" wato coal city. Bugu da kari yankin tayi fice matuka a noman hatsi kamar masara, da kuma doya da rogo da dai sauransu. Har wayau akwai manya-manya kasuwanni a garin kamar "kasuwar Kenyatta" da kuma "kasuwar Mayor".
Enugu ta kudu karamar hukumace dake jihar Enugu kuma tana da alhakin gudanarwa a tsakanin kauyukan dake karkashinta. Hon. Monday E. Eneh ne chiyaman na karamar hukumar tare da Hon. Sandra Akuabata Onyia a matsayin mataimakiyarsa da kuma Rt. Hon. Onyemaechi Ani a matsayin alkalin karamar hukumar Enugu ta kudu.[5]
Enugu ta Kudu na da wadannan gundumomi kamar haka;
Yankin karamar hukumar Enugu ta kudu tana da unguwanni kamar haka;[6]
s/n | Ugwuaji | Amechi-Uwani | Akuke | Obeagu |
---|---|---|---|---|
1. | Amuzam | Amagu | Amagwu | Amagu |
2. | Isiagu | Aukunanaw | Atagwu | Amauzam |
3. | Ndiaga | Isiagu | Okwu/Obeahu | Ngine |
4. | Ochufu | Iside | Umuanigu Ugwu | Nkpofia |
5. | Onuba | Ndiaga | Umuatogba-Owa | Obinagu |
6. | Ugboba-Ani | Ndiagbana | - | Obodou Vulu |
7. | Umunnaji Ngene | Ndiugbo | - | Uzamagu |
8. | Umunnaugwu | Sata | - | Uzamdun |
9. | - | Ugwafa | - | - |
10. | - | Ugwuagba | - | - |
11. | - | Umuedeachi | - | - |
12. | - | Umunugwu | - | - |
13. | - | Umuogo | - | - |
Mafi akasarin mutanen karamar hukumar Enugu ta kudu kiristoci ne.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.