yankin maraya a jamhuriyar Nijar From Wikipedia, the free encyclopedia
Dogondoutchi ko Dogonduci[1] (Dogon Dutse a Hausa ta mutanen Najeriya) birni ne dake kilomita 300 daga gabashin birnin Niamey na kasar Nijer, kuma kilomita 40 daga iyakar Nijar da Najeriya. Birnin na kan babbar hanyar da ta hada baban birnin kasar da Maradi da Zinder har zuwa gabashi da Arewacin yankunan Tahua, Agadez da Arlit. Dogondoutchi cibiyar gudanarwa ta yankun rayawa na Dogondoutchi a Jamhuriyar Nijar. Yana kuma karkashin jahar Dosso kuma. Al'umar yankin zaikai kimanin 80,000.
Dogondoutchi | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Jamhuriya | Nijar | |||
Yankin Nijar | Yankin Dosso | |||
Department of Niger (en) | Dogondoutchi (sashe) | |||
Babban birnin | ||||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 71,692 (2012) | |||
Labarin ƙasa | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Dallol Maouri (en) | |||
Altitude (en) | 227 m | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Daga Arewacin garin Dogondoutchi akwai manyan tsaunuka wanda daganan ne ma garin ya samo asalin sunan sa. Sannan kuma garina yana gefen kogi ne. Sannan garin yana a Kudu maso gabashin Nijar ne tsakanin Sahel da kudu yankin da ake samun wadataccen ruwan sama.
Akwai yanayin samun isasshen ruwan sama a yankin .
Akwai mutane kimanin 80,000 (kidayar 2011) akwai akalla mutane 30,000 a yankin birni. Akwai yankunan rayawa guda 11 da kauyuka 17 da kabilun Fulani 5. Kabilin yankin sun hada da Hausawa da Fulani da Abzinawa da Djerma (zabarmawa). Dogondoutchi shine mahadar yamma ta al'umar Hausawa sosai, wadanda sune kabilu mafiya yawa a yankin.
Kaso 90% na mutanen Musulunci ne addinin su, sai kuma masu bin addinin gargajiya kamar Bori na wadansu Hausawa. Sannan kuma akwai adadin masu bin Kirista kalilan a birnin.
A shekarar 2015 Dogon Dutsi tana da asibitin gunduma guda daya (1), cibiyar kula da uwa da yara kanana da tsofafffi guda daya (1), hadaddun cibiyoyin kiwon lafiya guda uku (3) da kuma dakunan shan magani da aka rarraba a kauyukan kewaye da birnin guda bakwai (7). Bacin wadannan akwai ma'aikata kamar likitoci 3, ma'aikatan jinya 14, ungozomomi 6, matkuna guda 4, shagunan sayar da magani (farmasi) 4 da wuraren ajiye magunguna guda 2. Yawancin haihuwa suna faruwa ne a cibiyoyin kiwon lafiya, abinda ya rage mace-macen mata da yara.[2]
Ana magana da yarukan Afirka guda 10 kowace rana a Nijar, aƙalla huɗu daga cikinsu ana anfani dasu a cikin Dogon Dutsi. Amma Faransanci shine harshen hukuma; wannan shine dalilin da ya sa ake fara koyawa yara Faransanci daga shekarar farko ta makarantar firamare inda suke share shekaru 6 na firamare suna amsar ilimi cikin yaren na Faransanci, za a ci gaba har zuwa karshen sakandare ana ba da koyarwa gaba ɗaya cikin Faransanci. A sherkarun 2015-2016, akwai makarantatun firamare na gwamnati guda 67 inda daya (1) daga cikinsu ta Franco-Arab (Faransanci-Larabci) ce; kuma azuzuwa kimanin 299 ne dalibai kusan 36 959 inda mata 17 597, maza 19362.[3]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.