From Wikipedia, the free encyclopedia
Damboa ƙaramar hukuma ce dake Jihar Borno Nijeriya. H Shelkwatar ƙaramar hukumar na nan ne a cikin garin Damboa. Tana da girman ƙasa kimanin 6,219 km² da kuma yawan jama'a da suka kai 233,200 tun daga alƙaluman ƙidayar shekara ta 2006.[1]
Damboa | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jiha | Jihar Borno | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 6,219 km² | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Lambar aika saƙo zuwa ƙaramar hukumar ta postal itace 601.[2] Asalin mazauna ƙaramar hukumar Damboa sune Mutanen Marghi, amma saboda haɓakar tattalin arziki Damboa ta hanyar sana'ar kamun kifi a wancan lokaci yasa aka samu mutanen Kanuri da wasu suke yawan kai komo a Damboa har yakai ga sun zama mazauna garin da auren matan garin Damboa. Hakan yasa a, yawancin mutanen Damboa akasarin su rabi Kanuri ne kuma rabi Marghi, dukda haka dai har yanzu akwai gidajen Marghi tsantsa waɗanda basu cuɗanya ba. Sanadiyar cuɗanyar al'ada a garin yasanya yawancin ƴan'asalin garin Damboa sunfi son jingina su da Marghi wasun su kuma Kanuri, amma dai ayau a Damboa akwai mutanen Marghi waɗanda sune ke da rinjaye da kuma mutanen Kanuri waɗanda suke binsu kuma suna zaune a garin kansu ɗaya.[1]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.