From Wikipedia, the free encyclopedia
Cututtuka da yawa suna yaduwa ne ta hanyar Iska inda kwayoyyi cutar su kan bi Iska ne domin su yadu.[1] Irin wadannan cututtukan suna da mutukar tasiri a fanin kiwon lafiyar Dan Adam da kuma dabbobi. Kwayoyin cutar za su iya zama kwayar halittar virus, bacteria ko kuma gansakuka. Akan yada su ne ta hanyar numfashi, magana, tari, atishawa ko kuma tada kura, feshin magunguna ko kuma sinadaren wanke bandaki.
Cutar dake yadu wa ta iska | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | infectious disease (en) |
Has immediate cause (en) | airborne transmission (en) |
A mafi yawan lokuta kwayoyin cutar na kawo gyanbo a cikin hanci, makogwaro ko kuma hunhu inda suke jawo tari, toshewar numfashi, ciwon makogwaro da kuma wasu matsalolin a jiki.
Cututtuka da yawa akan kamu da su ne ta hanyar Iska misali Corona virus, kyanda, bakon dauro, Yan rani[2],sarkewar numfashi, ciwon tarin fuka ko mura da mashako.[3] Mafi yawancin wadannan cututuka na bukatar amfani da naurar ventilator wajen jinyar su.
Cututtukan da muke kamuwa dasu ta hanyar gurbatacciyar Iska wadda ke dauke da kwayoyin cuta akan same su ne idan gurbatacciyar Iska dauke da kwayoyin cutar daga Mara lafiya ta hadu da mutum mai lafiya, ko kuma yawun sa, ko najasar sa, ko atishawar sa dauke da yawu ta fada kan mai lafiya. Misali, atishawa daga Gaban motar bus ta kan isa har bayan motar.[4]
Shakar kwayoyin cuta ta hanyar numfashi kan jawo rurucewar hanyar shakar Iska inda hakan ka jawo matsalar numfashi.Yawncin cututtukan numfashi na Dan Adam ba shakar sinadarai ne ke kawo su ba amma kuma hankan na tasiri wajen matsalar numfashi kamar cutar sarke war numfashi watau cutar Asthma.[5]
Cuttukan da ke yaduwa ta Iska kan shafi dabbobin gida kamar su kaji, agwagi, talotalo. Misali cutar Newcastle ta tsuntsaye.[6]
Akan kamu da cuta ne Idan mai lafiya ya shaki sinadari, ko ya shiga idanuwan sa ko hancin sa ko bakin sa [7] [8] . Ba wai sai mai lafiya yayi cudanya da mara lafiya gaba da ga ba, amma yanayi na zafi ko laima ko rashin wadatacciyar Iska duk sukan sa a kamu da cutar numfashi [8] .
Wasu daga cikin hanyoyin Riga kafi sune yin allurar lamba ko kuma Riga kafin cutar, sa takunkumi na fuska, da kuma yin nesa da Wanda ya kamu da cutar. Yin cudanya da mai cuta ba dole ne yasa mutum ya harbu ba. Kamuwa da cutar ta hangar Iska ya danganta da karfin garkuwan jiki da mutum yake dashi ko kuma yawan kwayoyin cutar da mutum ya shaka.[11]
Akan yi amfani da magungunan kashe cututtuka wajen maganin cutar sanyi ta sarkewar numfashi ko ciwon madaukai.[12]
Da yawa daga cikin masana kiwon lafiya sun bada shawarar yin nesa da juna a matsayin hanyar rage kamuwa da cutar da Iska ke yadawa.[13]
Za a iya rage kamuwa da cututtukan da Iska ke yada wa ta hanyar daukar wadannan matakai:
kada a rika yawan taba Baki ko hanci ko idanuwa da hannu ko kuma yin musabiha ko gaisuwar hannu ko sumbatar jama'a.[14]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.